Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-14 20:50:54    
Tsarin harkokin siyasa na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Danladi Iro Bambale, mazaunin birnin Zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. a cikin wasikar da ya aiko mana, ya yi mana tambayoyi da yawa dangane da tsarin siyasa na kasar Sin. Ya ce, yaya tsarin harkokin jam'iyyun siyasa yake a kasar Sin? Shin a kasar Sin ma'aikata da sarakunan gargajiya suna shiga harkar siyasa? Bayan wadanne shekaru ne ake zabe a kasar Sin? Yaya tsarin rarraba madafun iko yake a kasar Sin? wato daga gwamnatin tsakiya zuwa karamar hukuma?

Domin amsa tambayoyin, yanzu bari in dan bayyana muku tsarin harkokin siyasa na kasar Sin. Tsarin majalisar wakilan jama'a ya kasance tamkar tushe na tsarin siyasa na kasar Sin, wanda ya sha bamban da irin majalisun da ke karkashin tsarin siyasa na kasashen yammaci na raba ikon mulki da kafa doka da kuma shari'a, kuma tsarin mulkin kasar Sin ya tanada cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin hukuma ce ta koli ta kasar Sin. Bayan haka, tsarin gama kan jam'iyyu da dama da ba da shawara kan harkokin siyasa da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wani babban tsarin siyasa ne na kasar Sin. Ya kasance da jam'iyyu da dama a kasar Sin, ban da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke kan kujerar mulki, akwai sauran jam'iyyu guda takwas irin na dimokuradiyya. Wadannan jam'iyyun dimokuradiya ba jam'iyyun adawa ba ne, a maimakon haka dai, su jam'iyyu ne da ke shiga harkokin siyasa, kuma muhimman ayyukan da suke yi a fannin harkokin siyasa su ne: shiga shawarwarin da ake yi dangane da tsara manyan manufofin kasa da zaben shugabannin kasa, sa'an nan su sa hannu wajen kula da harkokin kasa da kuma aiwatar da manufofi da dokoki. A yayin da za a dauki manyan matakai ko kuma tsai da kuduri kan manyan harkokin kasa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kan yi shawarwari tare da 'yan jam'iyyun dimokuradiyya da kuma mutanen da ba su cikin ko wace irin jam'iyya ba, don sauraron ra'ayoyinsu da kuma shawarwarinsu tukuna, sa'an nan a tsai da kuduri.

Game da tambayar shin a kasar Sin ma'aikata da sarakunan gargajiya suna shiga harkar siyasa, to, hakika, sakamakon juyin juya hali da aka yi a shekara ta 1911 a karkashin jagorancin marigayi Sun Yat-sen, an hambarar da mulkin daular Qing na tsawon shekaru fiye da 200, haka kuma an kawo karshen tsarin sarakunan gargajiya na kasar Sin wanda ke da tsawon tarihi na sama da shekaru 2000, shi ya sa yanzu babu sarakunan gargajiya a nan kasar Sin, amma dukan jama'ar kasar Sin wadanda shekarunsu suka kai 18 suna da ikon zaben wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma shiga zaben zama wakilin.

Sa'an nan, game da yaya tsarin rarraba madafun iko yake a kasar Sin? Da farko, muna so mu bayyana muku cewa, ko da yake ya kasance da majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin da kuma majalisun wakilan jama'a na wurare daban daban a nan kasar Sin, amma babu maganar rarraba iko a nan kasar, sai dai danka iko a hannun majalisun wurare daban daban da majalisar wakilan jama'ar duk kasa ta yi idan ta ga ya dace, wato a karkashin jagorancin majalisar wakilan jama'ar duk kasa ne majalisu na wurare daban daban suke. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ikon kasa ya fito ne daga dukan jama'ar kasar Sin, shi ya sa ba zai yiwu ba a rarraba shi. Amma sabo da kasar Sin kasa ce mai girma, ga shi kuma da mutane masu dimbin yawa, sa'an nan zaman al'umma da tattalin arziki na wurare daban daban suna bunkasa cikin rashin daidaici, shi ya sa ba mai yiwuwa ba ne majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin ta kula da kome da kome, sai dai ta danka ikonta a hannun majalisun wurare daban daban, ta yadda za a gudanar da harkoki kamar yadda ya kamata. Bayan haka, a kan gudanar da zaben majalisun wakilan jama'a na matsayin duk kasa da larduna da jihohi da birane a shekaru biyar biyar, kuma a kan gudanar da zaben majalisu na matakan kauyuka da garurruwa a shekaru uku uku. (Lubabatu)