Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-14 08:32:49    
Wasan kankara salo-salo na kasar Sin ya samu ci gaba daga duk fannoni

cri

A cikin `yan shekarun da suka shige,nune-nunen `yan wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace na kasar Sin ya kara jawo hankulan mutanen kasashen duniya a gun manyan gasannin da aka shirya.A gun zama na 6 na taron wasannin Asiya na yanayin sanyi da aka yi a birnin Changchun na kasar Sin kwanakin baya ba da dadewa ba,kungiyar `yan wasan kankara salo-salo na kasar Sin ta samu babban sakamako wanda ya fi nagarta a tarihinta,wannan ya nuna mana cewa,karfin kungiyar `yan wasan kankara salo-salo na kasar Sin ya kara karuwa a bayyane.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Ran 3 ga wata,aka kammala gasannin wasan kankara salo-salo na zama na 6 na taron wasannin Asiya na yanayin sanyi.A cikin gasannin da aka shirya,gaba daya kungiyar kasar Sin ta samu lambobin yabo 8 wato lambobin zinariya 2 da na azurfa 3 da kuma na tagulla 3.Game da wannan,babban malamin koyar da wasan na kungiyar wasan kankara salo-salo ta kasar Sin Yao Bin ya bayyana cewa,ya gamsu da wannan sakamako sosai,saboda wannan sakamako shi ne sakamako mafi nagarta da kungiyar kasar Sin ta samu a gun taron wasannin Asiya na yanayin sanyi a tarihinta.Yao Bin ya ce:  `A tarihinmu,ba mu taba samun lambobin yabo 8 ba,wannan ya nuna mana cewa,matsayin wasan kankara salo-salo na kasar Sin ya riga ya shiga wani sabon mataki wato ya dagu bisa babban mataki kuma daga duk fannoni.`

An yi mana bayani cewa,a cikin shekaru 10 da suka shige,kodayake `yan wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace na kasar Sin kamarsu Shen Xue da Zhao Hongbo da Pang Qing da Tong Jian da Zhang Dan da Zhang Hao da sauransu sun riga sun zama `yan wasa mafiya nagarta a duniya,amma a fannin wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace ne kawai.A takaice dai,ana iya cewa,kungiyar kasar Sin ba ta kai matsayin kungiyar kasar Japan ba.Amma yanzu,halin nan ya canja,musamman a gun wannan taron wasannin Asiya na yanayin sanyi, kungiyar wasan kankara salo-salo ta kasar Sin ta samu ci gaba ne daga duk fannoni,wato ta samu lambobin yabo na kowace gasa,wanda a ciki `yan wasan kasar Sin sun samu dukkan lambobin yabo na gasannin gaurayen namiji da mace,a karshe dai yawan lambobin yabo da ta samu ya fi lambobin yabo da kungiyar kasar Japan ta samu.

Ban da wannan kuma,malamin koyar da wasa Yao Bin ya fi mai da hankali kan wasan kankara na namiji,dalilin da ya sa haka shi ne domin a cikin `yan shekarun da suka shige,`yan wasan kankara na maza na kasar Sin ba su taba samun sakamako mai kyau ba.Amma a ran 3 ga wata,a cikin zagaye na karshe na gasar wasan kankara na maza,`dan wasa daga kasar Sin Xu Ming ya yi kokari kuma ya zama zakara ya samu lambar zinariya.Wani `dan wasa daga kasar Sin daban Li cheng Jiang ya zama lambatu.`Dan wasa daga kasar Japan Nakaniwa Kensuke ya samu lambatiri.Malam Yao Bin ya darajanta sakamakon da `dan wasa Xu Ming ya samu sosai,ya ce,  `Lallei Xu Ming ya yi kokari saboda bai taba shiga babbar gasa ta matsayin duniya ba a da,ana iya cewa,ya sha wahala kuma ya yi kokari sosai.`

Game da wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace,a kullum `yan wasan kasar Sin suna iya samun sakamako mai kyau,a gun wannan taron wasannin Asiya na yanayin sanyi,ba ma kawai `yan wasan kasar Sin sun samu lambar zinariya ta gasar wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace ba,har ma sun samu lambar azurfa da ta tagulla.Wannan ya inganta matsayin ci gaba na kungiyar kasar Sin a duniya.

Kodayake kungiyar wasan kankara ta kasar Sin ta riga ta samu ci gaba daga duk fannoni,amma `yan wasan kasar Sin sun gane cewa dole ne su ci gaba da sanya matukar kokari.Zakaran wasan kankara na maza na taron wasannin Asiya na yanayin sanyi na Changchun Xu Ming ya ce,  `Matsayin wasan kankara na maza na kasar Sin bai kai na kasashen Turai ba,daga fannin nune-nune da na fahimtar kide-kide da sauransu,kamata ya yi mu yi iyakacin kokari.`

Malami Yao Bin ya ce,nan gaba kungiyar wasan kankara salo-salo ta kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari saboda `yan wasan kasar Sin suna fatan za su samu lambar zinariya a gun taron wasannin Olimpic na yanayin sanyi da za a yi a Vancouver a shekarar 2010.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)