Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-14 08:30:24    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (07/02-13/02)

cri

Ran 8 ga wata,shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing na shekarar 2008 Mr.Liu Qi ya yi bayani kan aikin shirya taron wasannin Olimpic da birnin Beijing ke yi ga kwamitin zartaswa na kwamitin wasannin Olimpic na duniya wanda ke yin taro a birnin Lausanne na kasar Switzerland ta waya mai hoto,daga baya kuma shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogger da shugaban kwamitin sulhuntawa na zama na 29 na taron wasannin Olimpic na kwamitin wasannin Olimpic na duniya Hein Verbruggen sun bayyana cewa,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing yana gudanar da aikin shirya taron wasannin Olimpic yadda ya kamata kuma lami lafiya,kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya gamsar da aikin da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ke yi sosai.

Ran 6 ga wata,a gun zagaye na karshe na gasar gudun tsallake shinge na mita 60 ta gasar guje-guje da tsalle-tsalle da ake yi a cikin daki a birnin Duesseldorf na kasar Jamus,`dan wasa daga kasar Sin Liu Xiang ya sami lambawan bisa maki dakika 7 da 53,kuma ya karya matsayin bajimta na wannan taron wasanni cikin daki a wannan wasa.

Ran 8 ga wata,a gun gasar cin kofin nahiyoyi hudu na wasan kankara salo-salo na shekarar 2007 da ake yi a Colorado Springs,`yan wasa daga kasar Sin Shen Xue da Zhao Hongbo sun samu lambar zinariya ta wasan kankara salo-salo na gaurayen namiji da mace,`yan wasa daga kasar Sin Pang Qing da Tong Jian sun zama lambatu,`yan wasa daga kasar Amerka Rena Inoue da John Baldwin sun zama lambatiri.Gasar cin kofin mahiyoyi hudu ta wasan kankara salo-salo ita ce gasar kankara salo-salo mafi matsayin koli ta gargajiya a duniya.`Yan wasa da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 15 da yawansu ya kai 100 sun shiga gasannin da aka shirya wato na wannan shekara. (Jamila Zhou)