Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-13 21:24:38    
Birnin Manzhouli, wanda ke nuna sigogin musamman na al'adun kasar Rasha

cri

A kan manyan titunan birnin Manzhouli, ana iya ganin Rashawa a ko ina, sa'an nan kuma, ban da Sinanci, an kuma rubuta Rashanci da harshen Mongolia a kan allon kantuna iri daban daban, watakila mutane sun ji suna yawo a kasashen ketare. Madam Xin Mei, wadda ke aiki a cikin wani otel na birnin Manzhouli, ta gaya mana cewa,'Yanzu Rashawa da yawa sun zo birninmu na Manzhouli, musamman ma a lokacin hunturu, saboda bikin Kirsimati ya zo a watan Disamba, sun zo nan don sayen wasu kyaututtuka, a maimakon taya murnar wannan biki. Su kan sayi wasu kananan kayayyaki da tufafi da takalma da huluna da dai sauransu. Ana sayar da isassun wadannan kayayyaki iri-iri a kasar Sin.'

Ba kawai ana iya fahimtar sigogin musamman na kasar Rasha a tituna da unguwanni na Manzhouli ba, har ma yana kasancewa da wani dandalin da aka gina bisa halin da birnin Manzhouli ke ciki, ana kiransa 'Taowa', wato irin 'yar tsana ta musamman ta kasar Rasha, Turawa su kan kira ta Matryoshka. Dandalin Taowa dandalin yawon shakatawa ne kawai da aka gina bisa kayan fasaha na gargajiya na kasar Rasha wato Taowa, fadinsa ya kai misalin murabba'in mita dubu 60. Babban gininsa shi ne wata babbar 'yar tsana ta Taowa mai tsayin misalin mita 30, wadda ta fi tsayi a duniya a yanzu. A kewayenta kuma, akwai kanana fiye da 200, da kuma manyan kwayaye masu launuka daban daban 30 da aka yi don murnar sallar Easter a Turance, wadanda alamu ne na zumunci da kauna da kuma fatan alheri a kasar Rasha.

A lokacin hunturu, a kan yi wa birnin Manzhouli ado da kankara mai taushi. Yawan sanyi ya yi kasa da digiri 30 a karkashin sifiri da dare a waje, amma sanyi bai hana masu yawon shakatawa zuwa ba, kankara da kankara mai taushi sun jawo mutane da yawa don ziyarar birnin Manzhouli. A lokacin hunturu na ko wane shekara, a kan yi bikin kankara da kankara mai taushi a wannan birni, masu fasaha na kasar Sin sun sassaka mutum-mutumi iri daban daban da kankara da kankara mai taushi, wadanda suka hada da mashahuran mutane na kasar Sin da gine-ginen sauran kasashe. Sululun wasan yara da aka yi da kankara ya zama abin wasa ne mafi kyau ga yara a lokacin hunturu. Li Dongsheng, wani dan makarantar firamare ne a birnin Manzhouli, ya bayyana cewa, 'A gun bikin kankara da kankara mai taushi da aka yi a lokacin hunturu, ana wake-wake, ana rawa, an yi gine-gine daban daban da kankara, ban da wannan kuma, mun iya yin wasa da sululun. Sululun kayan wasa ne mai ban sha'awa ainun. Mutanenmu na kasar Sin da na kasar Mongolia da na sauran kasashen waje sun zo nan don yin ziyara da daukar hotuna.'

Bikin kaddamar da bikin kankara da kankara mai taushi sun fi jawo hankulan mutane, a ko wace shekara war haka, masu yawon shakatawa na gida da na kasashen Rasha da Mongolia sun halarci wannan kasaitaccen biki. Ban da kallon kyawawan mutum-mutumin da aka yi da kankara da kankara mai taushi, su kan ji dadin ganin nagartattun wasannin da masu fasaha na wadannan kasashe 3 suka nuna. Nastya, wata budurwa ta kasar Rasha da ta zo nan don kallon wannan bikin. Ta ce, 'Ina sha'awar mutum-mutumin da aka yi a kankara mai taushi, wasannin da aka nuna na da kyau sosai. Yawan mutanenmu na kasar Rasha da suka halarci bikin kankara da kankara mai tashi yana karuwa a ko wace shekara. Bikin kankara da kankara mai taushi da aka yi a nan ya ba da babban tasiri a kasar Rasha.'

Bayan fahimtar sigogin musamman na biranen da ke da salon kasar Rasha da kuma ganin gagarumin bikin kankara da kankara mai taushi, kada a manta da sayen kananan kayayyaki tamkar abubuwan tunawa kafin a koma gida.

Shiyyar cinikayya ta hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha da gwamnatin Sin da Rasha suka kafa tare a Manzhouli wuri ne mai kyau ga mutanen Rasha a fannin sayen kayayyakin kasar Sin, inda ake sayar da isassun ire-iren kayayyaki. Haka zalika kuma, akwai kasuwoyi da yawa a cikin birnin Manzhouli, inda mutanen Sin da na sauran kasashen duniya suke iya sayen kananan kayayyaki da yawa da aka kera a kasashen Rasha da Mongolia.

Kamar yadda muka ambata a baya, birnin Manzhouli birni ne da ke nuna sigogin musamman na kasashen Sin da Rasha tare, ziyararsa ta yi kama da kai wa wata kasa ziyara, ma iya cewa, yana daya daga cikin kananan birane masu dacewa da ziyara a kasar Sin.