Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-13 21:18:20    
Kara cin kayayyakin lamba ga tsofaffi zai iya saukaka cutar tabarbarewar kwakwalwa

cri

Kwararru masu ilmin aikin likitanci na kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga tsofaffi wajen dangantakar da ke tsakanin kayayyakin lambu da tabarbarewa, daga baya kuma sun gano cewa, kara cin kayayyakin lambu zai ba da taimako wajen hana tabarbarewar kwakwalwa, ta yadda za a iya saukaka lalacewar tunani wanda tabarbarewar kwakwalwa ke haddasawa.

Manazarta na jami'ar Rush da ke birnin Chicago na kasar Amurka sun buga wani labari a kan mujallar ilimin nazarin jijiyoyin dan Adam, inda suka nuna cewa, sun gudanar da wani bincike na tsawon shekaru shida ga tsafaffi maza da mata 2000 wadanda shekarunsu ya zarce 65 da haihuwa kan abincin da su kan ci. Daga baya kuma sun gano cewa, tabarbarewar kwakwalwar tsofaffin da su kan ci kayayyakin lambu a ko wace rana ta ragu da kashi 40 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su ci kayayyakin lambu ko kadan ba.

A cikin kayayyakin lambu iri daban daban, wadanda suke da koren ganye sun fi ba da kariya ga lafiyar dan Adam. Manazarta sun bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kayayyakin lambu da ke da koren ganye suna kunshe da bitamin E mai yawa wanda zai ba da taimako sosai ga lafiyar jikin dan Adam. Ana ganin cewa, bitamin E yana iya taimakawa wajen hana lalacewar kwayoyin jikin dan Adam, ta yadda zai iya saukaka cutar tabarbarewar kwakwalwa.

Malam Claire Mirrlees, mai kula da wannan bincike ya bayyana cewa, 'ya'yan itatuwa su ma suna kunshe da bitamin E, amma ya yi kadan idan an kwatanta shi da wanda ke cikin kayayyakin lambu. Bugu da kari kuma, cin kayayyakin lambu bayan da aka dafa su tare da man zaitun zai ba da taimako ga jikin dan Adam wajen karbar bitamin E. Haka zalika kuma kitsen da ke cikin man kayan lambu zai ba da taimako wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu, ta yadda za a ba da taimako wajen kiyaye lafiyar kwakwalwa.

Yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani game da 'ya'yan 'yan kwadago manoma. A wadannan shekaru fiye da 20 da suka gabata, an raya tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, haka kuma tare da bunkasuwar birane da masana'antu, manoma masu yawa sun je biranen da ke yankuna masu ci gaba na kasar Sin domin neman samun aikin yi. Wannan kuwa ya haddasa wasu matsaloli a jere, alal misali, ko yaya 'ya'yan 'yan kwadago manoma za su iya samu ilmi? Kuma yaya za su iya girma a cikin yanayi mai kyau? To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda kasar Sin take yi wajen kyautata yanayin karatu na 'ya'yan 'yan kwadago manoma.