Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-13 21:32:12    
Kasar Sin ta samu sabon cigaba wajen yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci

cri
A ran 13 ga wata, Mr. Gan Yisheng, kakakin kwamitin ladabtarwa da da'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana a birnin Beijing cewa, a shekarar 2006, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke kan mukamin mulkin kasar Sin ta samu sabon cigaba da sakamako wajen samar da tsabtatattun jami'ai kuma masu gaskiya da yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci, musamman ta sami cigaba sosai wajen jaddada da'a cikin jam'iyyar da gwamnati da gano jami'ai masu cin hanci da mutane masu cin rashawa lokacin da ake yi harkokin kasuwanci da kuma yaki da harkoki marasa adalci da suke bata moriyar jama'a.

A gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudunarwa ta kasar Sin ya shirya a wannan rana, Mr. Gan Yisheng ya ce, "Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin suna mai da hankali sosai a kullum wajen yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci ba tare da boye kome ba. Aikin yin yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci muhimmin aikin siyasa ne da ke bisa wuyan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin domin yana shafar kasancewa da cigaban jam'iyyar har da duk kasar Sin gaba daya."

Mr. Gan ya bayyana cewa, a shekarar 2006, yawan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi musu hukunci ya kai fiye da dubu 97. Dalilan da suka sa aka yi musu hukunci su ne, suna bata odar zaman lafiya, ko ba su yi aikinsu bisa doka ba, har ma wasu sun karya dokokin da'a da na kudi. A waje daya kuma, an kai jami'ai 7 wadanda suke kan mukamin gwamnoni ko ministoci na larduna da gwamnati zuwa hukumomin shari'a. Abin musamman da ya kamata mu ambata shi ne, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi bincike kan batutuwan da suke karya dokoki da Chen Liangyu, tsohon sakataren kwamitin birnin Shanghai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi. Wannan ya tabbatar da cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da niyya mai karfi wajen yin yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci. Mr. Gan Yisheng ya ce, "Bisa kididdigar da aka yi, tun daga shekarar 2003, sabo da hukumomin da'a da bincike na matakai daban-daban na kasar Sin suna kara daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci, yawan irin wadannan matsalolin da aka gano yana ta raguwa a kowace shekara. A shekarar 2006, yawan irin wadannan matsalolin da aka gano ya ragu da kashi 10.9 cikin kashi dari bisa na makamacin lokaci na shekarar 2005. "

A shekarar 2006, muhimmin halin musamman da kasar Sin ke ciki wajen yaki da cin hanci da al'amubazzaranci shi ne, bayan da aka kara yin bincike kan wasu matsaloli, an gano wasu jami'ai wadanda suka ci hanci kuma suka buya sosai a wasu larduna da birane inda ba a gano muhimman jami'ai wadanda suke kan mukamin gwamna kuma suka karya dokoki a cikin 'yan shekarun da suka wuce ba. Lokacin da ake binciken wadannan matsaloli, wasiku da sakwannin da jama'a suka aika wa kwamitin ladabtarwa da da'a na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa kwarai. Sabo da haka, Mr. Gan Yisheng ya bayyana cewa, "Mun gano wasu muhimman matsalolin ci hanci da rashawa da al'amubazzaranci ta hanyoyin karbar ziyarce-ziyarcen da jama'a suka kawo mana da samar da lambobin waya ko bude shafin internet ga jama'a domin karbar labarun da suke gabatarwa game da irin wadannan matsaloli. Bugu da kari kuma, mun kara sa ido kan aikin binciken irin wadannan matsaloli."

A waje daya kuma, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen gano matsalolin cin hanci da rashawa lokacin da ake yin harkokin kasuwanci. A shekarar 2006, hukumomin shari'a da hukumomin aiwatar da dokoki na matakai daban-daban na kasar Sin sun dauki matakai daban-daban wajen yaki da matsalolin da ke bata odar yin harkokin kasuwanci domin kare ainihin moriyar jama'a. Yawan matsalolin cin hanci da rashawa da suke shafar yin harkokin kasuwanci da aka gano ya kai fiye da dubu 10. Yawan kudin da wadannan matsaloli suka shafa ya kai dalar Amurka kimanin miliyan 470.

Bugu da kari kuma, Mr. Gan Yisheng ya ce, ko da ya ke kasar Sin ta samu cigaba sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci, amma aikin yin yaki da irin wadannan matsaloli ya yi tsanani har yanzu a wasu fannoni. Mr. Gan ya ce, "Ba za mu musunta ba, har yanzu kuma a cikin dogon lokaci mai zuwa ne kasar Sin za ta ci gaba da zama a cikin matakin farko na zaman gurguzu. Sabo da har yanzu ba mu da cikakkun tsarin kasa da dokoki da hukumomin gwamnati, ba zai yiyuwa mu iya kawar da matsalolin cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci gaba daya. Amma muna cike da imani cewa, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin, za a kara samun cigaba wajen yin yaki da cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci a kasar Sin." (Sanusi Chen)