Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-12 18:45:23    
Takaitaccen bayani game da kabilar Jinuo

cri

'Yan kabilar Jinuo suna kiran kansu Jinuo. Ma'anar Jinuo cikin yaren Jinuo ita ce, "zuriyoyin Kawu" ko "Al'umma ce da ke girmama Kawunai". Jama'ar kabilar Junuo suna zama a kudancin lardin Yunnan. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Junuo ya kai misalin dubu 20. Suna da yaren Jinuo, amma babu kalmomi ko haruffai.

Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, 'yan kabilar Jinuo suna cikin karshen lokaci na zaman al'umma mai duhun kai.

A da, mutanen kabilar Jinuo sun yi aikin gona da wuka da wuta kawai. Muhimman shuke-shuke da 'ya'yan itatuwa da suka noma suna kunshe da shinkafa da masara da auduga da ayaba da gwanda da kuma shaye-shaye. Dabbobin da suke kiwo suna kunshe da shanu da bakwane. Amma sun kiwo shanu da bakwane ba domin yin noma ba, sai domin sadakar da biki da samar da naman ci. A waje daya kuma, suna kiwon sauran dabbobin gida da na tsuntsaye.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, al'ummar Jinuo ta shiga zaman al'ummar gurguzu. Yanzu an riga an gina dam domin samar wa mutanen kabilar Jinuo wutar lantarki. Sa'an nan kuma, yanzu 'yan kabilar Jinuo ba su yin aikin gona da wuka da wuta ba, amma suna amfani da injuna da na'urorin zamani. Sakamakon haka, zaman rayuwar mutanen kabilar Jinuo yana kuma samun kyautatuwa. Bugu da kari kuma, yawancin yara sun samu damar shiga makaranta. Har ma wasu matasa sun ci jarrabawa sun yi karatu a jami'o'i da kwalejoji. A waje daya kuma, an riga an bude dakunan likitanci da asibiti a yankunan kabilar Jinuo domin tabbatar da koshin lafiyarsu.

Kabilar Jinuo tana da al'adu iri iri ciki har da tatsuniyoyi da almara da wakoki da kide-kide da bushe-bushe da raye-raye iri iri. Bugu da kari kuma, jama'ar kabilar Jinuo suna da fasahar saka kayayyaki da gora.

Bisa al'adar kabilar Jinuo, kowane saurayi yana iya auren mace daya kamar yadda sauran kabilun kasar Sin suke yi. Kafin a yi bikin aure, samari da 'yan mata suna da 'yancin yin soyayya. Bayan da wani saurayi da wata mace suka fada cikin kogin soyayya, za su iya zama tare. Za a yi musu bikin aure bayan da mace ta haihi jaririn farko. Lokacin da ake shirya bikin aure, dole ne dattawa su je wajen bikin.