Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-12 15:36:50    
Ko sabon kwamandan sojojin Amurka da ke Iraqi zai iya daidaita rikicin da ake yi a Iraqi ko a'a?

cri

Kwanan baya, sabon babban kwamandan sojojin Amurka da ke kasar Iraqi Mr. David Petraeus ya karbi ragamar aiki, ya zama kwamandan sojojin Amurka da ke Iraqi na uku. A gun bikin hawa kan karagar mulki da aka shirya a sansanin sojojin Amurka da ke Bagadaza, ya bayyana cewa, zai canja manyan tsare-tsare, da dabarar sojojin Amurka, da shugabanci matakan da sojojin kasar suke yi a Iraqi bisa sabon tunani, da kuma yin amfani da damar da aka samar, ta haka za a canja matsanacin halin da kasar Iraqi ke ciki. Amma, yawancin mutane suna shakka kan ko zai iya cika alkawarinsa ko a'a.

Mr. Petraeus, wanda shekarunsa na haifuwa ya kai 54, wani leftanar janar ne, kuma shehun malami ne wajen kimiyyar huldodin kasashen duniya, bisa matsayinsa na shugaban rundunar sojojin kundunbala ne, ya taba halartar ayyukan soja da kasar Amurka ta dauka a shekarar 2003, domin hambarar da mulkin Sadam. Daga baya, ya taba kula da aikin horar da sojojin tsaron kai na Iraqi. Bayan haka kuma, ya taba hada kai da shugabanni na birnin Mosul da ke arewancin kasar Iraqi, kuma sun kyautatta halin tsaron kai da shiyyar ke ciki cikin nasara. Ba kamar yadda George Casey, wato tsohon babban kwamandan sojojin Amurka ya yi a kasar Iraqi ba, Mr. Petraeus ya jaddada cewa, tilas ne kasashen Amurka da Iraqi su karfafa hadin kansu, domin hana miyagun ayyuka na nuna karfin tuwo, ya kamata su "dauki nauyin bisa wuyansu tare".



A ranar da Mr. Petraeus ya karbi mulki, ya bayyana cewa, zai dauki sabbin manyan tsare-tsare, da dabara kan rikicin da ake yi tsakanin rukunonin addinai a kasar Iraqi. Wasu suna ganin cewa, wadannan dabaru sun hada da abubuwa kamar haka: da farko, mazaunan wurare daban daban na kasar Iraqi suna da katin shaida da ke hada da wasu labarun halittu, wato sai da katin nan ne mutane ke iya shiga wuraren da ke kasar Iraqi; na biyu, sojojin Amurka ba za su koma sansanoni ba, bayan da suka sassauta miyagun ayyukan nuna karfin tuwo kamar yadda su kan yi a da, za su kafa wasu kananan sansanoni a shiyyoyin da aka fi samun tsananan rikici a tsakanin rukunonin addinai, kuma za su yi hadin kai tare da al'umomi na wuraren cikin dogon lokaci, da kuma yin sintiri a inda kusa da su. Sabo da haka, za a raba Bagadaza kamar yankuna 9, 'yan sanda da sojijin tsaron kai na kasar Iraqi, wadanda suke zaune a sansanoni kamar 30 za su dauki matakan tabbatar da zaman lafiya a karkashin sa idon sojojin Amurka.

Amma, manazarta suna ganin cewa, ko yaya za a canja manyan tsare-tsare da dabara, ba za a warware muhimman matsaloli ba. A kalla dai Mr. Petraeus yana fuskantar kalubale daga fannoni 3:



Da farko, yaya za a daidaita dangantakar da ke tsakanin darikar Suni, da darikar Shi'a, wannan ita ce matsalar mafi tsanani. Ko da ya ke gwamnatin Iraqi da ke karkashin shugabancin Mr. Nouri al-Maliki, firayin ministan kasar ta yi alkawarin cewa, za ta wargaza dakarun nan biyu kwata kwata, amma ana kasancewa da bambanci sosai a tsakaninta da bangaren Amurka. Kullum bangaren Amurka yana zargin gwamnatin Iraqi, sabo da ba ta dauki matakai masu dacewa ba wajen murkushe dakarun darikar Shi'a da ke hade da sojojin Mahdi; amma 'yan darikar Shi'a tana bukatar bangaren Amurka da ya mai da dakarun darikar Sunni su zama wani muhimmin burin da zai murkushe, a lokacin da ya kai bugu ga kungiyar Al-Qaeda.

Na biyu, ko sojojin hadin kan Amurka da Iraqi za su kara yawan sojoji, don yin sintiri, ko su yada katin shaida masu hade da labarun halittu, dukansu ba za su iya tabbatar da kuma murkushe wadannan masu laifi ba, kuma ba za su hana faruwar lamarin kai farmaki a hakika ba.

Na uku, mutanen Amurka da ke adawa da manufar da gwamnatin Bush ke dauka a Iraqi suna ta karuwa, sabo da ana ta yin yakin Iraqi kusan shekaru 4, sojojin Amurka fiye da dubu 3 da dari 1 sun mutu, kuma yawan kudin da kasar Amurka ta kashe kan yakin ya kai dollar Amurka biliyan daruruwa. A cikin halin da rashin goyon baya daga jama'ar kasar Amurka, ko da ya ke Mr. Petraeus yana da kwarewa sosai, amma da kyar ya sassauta rikicin da ake yi a tsakanin Iraqi cikin nasara.  (Bilkisu)