Bayan da ya kammala ziyarar aiki a kasashe 8 na Afirka, shugaba Hu Jintao na kasar Sin tashi daga kasar Seychelles a ran 10 ga wata da dare bisa agogon wurin. Shugaba Hu ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai wa kasashe 8 na Afirka ya ci cikakkiyar nasara.
Shugaba Hu Jintao ya dauki kwanaki 11 yana kai wa kasashen Kamaru da Liberia da Sudan da Zambia da Nambia da Afirka ta Kudu da Mozambique da Seychells ziyarar aiki, tsawon ziyararsa ya kai misalin kilomita 40,000. Game da ziyarar da ya kai wa Afirka a wannan karo, shugaba Hu ya yi bayanin cewa,'Na yi kwanaki 11 ina kai wa kasashe 8 na Afirka ziyara, na sha aiki sosai a kan hanyata. Shugabannin wadannan kasashe 8 da sauran shugabanninsu da ni mun yi shawarwari a tsakaninmu, inda muka yi musayar ra'ayoyinmu kan kara raya dangantakar da ke tsakanin kasashenmu da aiwatar da sakamakon taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka da wasu al'amuran duniya da na shiyyoyi da ke jawo hankulanmu duka, mun kuma sami ra'ayi daya a fannoni da yawa. Bangarorinmu 2 mun kuma daddale takardun da suka shafi yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki da al'adu da kiwon lafiya da aikin gona. Ban da wannan kuma, na ba da jawabi domin dukan kasashen Afirka a jami'ar Pretoria ta kasar Afirka ta Kudu, inda na gabatar da cewa, ya kamata a kara yin mu'amala a tsakanin matasan Sin da Afirka, da zurfafa zumuncin gargajiya da habaka hadin gwiwa da kuma yin kokari wajen bunkasa dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. Ziyarar da na yi a wannan karo ta ci cikakkiyar nasara.'
A farkon sabuwar shekara, shugaba Hu Jintao ya kai wa kasashe 8 na Afirka ziyara.
Wadannan kasashe 8 suna nuna kyakkyawar fata kan raya zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka. A lokacin da shugaba Hu yake ziyara a kasashen 8, sun bai wa shugaban Hu girmamawa sosai, sun kuma ba shi hidimomi mafi kyau.
A gun bukukuwa fiye da 90 da aka yi, shugaba Hu ya yi magana kan zumuncin da ke tsakanin Sin da Afikra, da hadin gwiwar moriyar juna, da yin mu'amalar al'adun mutane, da neman samun ci gaba tare, dukansu sun nuna cewa, rangadin sada zumunci da hadin gwiwa da shugaba Hu ya yi a wannan karo na da ma'ana mai zurfi.
Shirye-shirye da matakai a jere da shugaba Hu ya gabatar da su a lokacin ziyararsa sun shaida cewa, kasar Sin tana cika alkawarin da ta yi, tana kokarin samun sakamako mai kyau, tana yin hadin gwiwa da kasashen Afirka bisa ka'idar yin zaman daidai wa daida cikin sahihanci.
Don kyautata tsarin ciniki a tsakanin Sin da Afirka da kuma daukaka ci gaban ciniki a tsakanin Sin da Aifrka cikin daidaito, a bayyane ne shugaba Hu ya ce, gwamnatin Sin ba ta sa kaimi kan masana'antunta da su mamaye kasuwoyin sauran kasashe ta hanyar kara fitar da kayayyaki kawai, a maimakon haka, za ta kara shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka, da rage da soke makudan kudaden kwastan kan wasu kayayyakin da aka saya daga kasashen Afirka don sassauta damuwar da wasu kasashen Afirka suka nuna kan batun ciniki.
Shugabannin kasashen 8 na Afirka dukansu sun darajanta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka da kuma dangantakar da ke tsakanin kasashensu da kasar Sin.
Game da zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka, shugaba Hu ya yi bayanin cewa,'Tun da can har zuwa nan gaba, jama'ar Sin abokai ne ga jama'ar Afirka, wadanda suke yin zaman daidai wa daida, da amincewa da juna, su aminai ne da suke moriyar juna da hada kansu don cin nasara tare, su kuma 'yan uwa ne da ke shan wahala tare. Tabbas ne jama'ar Sin da Afirka za su sada zumunci a tsakaninsu daga zuriyoyi.'(Tasallah)
|