Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-11 18:40:03    
Hu Jintao ya kawo karshen rangadinsa na sada zumunta da hadin guiwa a kasashen Afirka 8

cri
A ran 10 ga wata, a lokacin da shugaban kasar Sin Hu Jintao yake kawo karshen rangadinsa na sada zumunta da hadin guiwa a kasashen Afirka 8, wato Kamaru da Liberia da Sudan da Zambiya da Namibiya da Afirka da kudu da Mozambique da Seychells, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya karbi ziyarar da manema labaru na kasar Sin suka kai masa, inda ya ce, ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi a wadannan kasashen Afirka 8 rangadi ne na sada zumunta da hadin guiwa ga kasashen Afirka duka, wannan kuma muhimmin al'amari daban ne da aka yi bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin guiwa tsakanin Sin da Afirka. Tabbas ne ziyarar za ta yi tasiri sosai ga makomar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Wadannan kasashe 8 da shugaba Hu Jintao ya kai musu ziyara suna yankuna daban-daban a duk nahiyar Afirka. Wadannan kasashe, ko manya ko kanana suna kan matsayi daban-daban wajen neman bunkasuwa. Sabo da haka, aka fadi cewa, wannan ziyara tana bayyana cewa, kasar Sin tana raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka daga duk fannoni tare da samfurori iri iri. A waje daya kuma, a karo na farko ne shugaban kasar Sin ya kai ziyara ga kasashe 6 daga cikin wadannan kasashe 8. A cikin kwanaki 11 da suka wuce, tsawon hanyar da shugaba Hu ya bi ya kai kilomita kusan dubu 40, ya yi shawarwari tare da shugabannin kasashen Afirka fiye da 20, ya kuma gana da sauran manyan mutane daruruwa na bangarori daban-daban na kasashen Afirka. Haka nan kuma, ya halarci bukukuwa har sau fiye da 90 tare da bayar da muhimman bayanai har sau 30 ko fiye. Li Zhaoxing ya ce, wannan ziyara ta samu muhimman sakamako da yawa daga fannoni daban-daban, sakamakon haka, ana bayyana cewa, wannan hakikar ziyara ce da ke sada zumunta da hadin guiwa.

Karfafa zumuncin gargajiya da jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka za su iya ci gaba da sada zumunta a tsakaninsu har abada, yana daya daga cikin makasudin wannan ziyarar da Hu Jintao ya yi.

Buri daban da shugaba Hu ya kai wa kasashen Afirka ziyara shi ne aiwatar da matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta gabatar a gun taron koli na Beijina na dandalin tattaunawar hadin guiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata domin kara yin hakikar hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da kuma goyon bayan yunkurin neman bunkasuwa da kasashen Afirka suke yi. Lokacin da shugaba Hu Jintao yake yin ziyara a wadannan kasashen Afirka 8, a cikin yarjejeniyoyin hadin guiwa fiye da 50 da aka kulla, galibinsu suna aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing. Sabo da haka, bi da bi ne shugabannin kasashen Afirka suka bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce da za a iya amincewa da ita. Kasashen Afirka suna fatan za a iya kara yin hadin guiwa a tsakaninsu da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari da ayyukan yau da kullum da dai makamatansu.

Li Zhaoxing ya kara da cewa, a cikin wannan ziyara, bangarorin Sin da Afirka sun samu kwatakwacin ra'ayi sosai kan yadda za a kara raya hadin guiwar sada zumunta daga duk fannoni da karfafa sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. A cikin ziyararsa, Hu Jintao ya ce, ya kamata kasashen Sin da Afirka su kara yin mu'ammala da yin koyi da juna da kuma neman bunkasuwa tare da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa tare domin kafuwar wata duniya mai jituwa wadda ke tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da neman bunkasuwar gaba daya. Shugabannin kasashen Afirka sun yaba wa manufofin da shugaba Hu ya gabatar wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Sun bayyana cewa, raya dangantakar da ke tsakaninsu da kasar Sin muhimmin zabe ne da kasashen Afirka suka yi bisa manyan tsare-tsarensu, yana kuma dacewa da halin da ake ciki da ainihin moriyar jama'ar kasashen Afirka.

A waje daya kuma, lokacin da yake yin ziyara a Afirka, shugaba Hu ya sanar da matsayi da matakan da kasar Sin ke dauka kan batutuwa iri iri ciki har da batun Darfur na kasar Sudan. Li Zhaoxing ya ce, wannan ya bayyana cewa, a sahihanci ne kasar Sin tana daukar matakan nuna wa kasashen Afirka goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya a Afirka, kuma tana goyon bayan kokarin da kasashen Afirka suke yi kan yadda za su iya hada da kuma dogara da kansu domin neman bunkasuwa mai dorewa da tabbatar da zamna lafiya har abada a duk fadin Afirka.

Li Zhaoxing ya ce, wannan rangadin sada zumunta da hadin guiwa ya cimma burin karfafuwar zumuncin gargajiya da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing da kara yin hakikar hadin guiwa domin neman bunkasuwa tare a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Tabbas ne wannan ziyara muhimmin al'amari ne a cikin tarihin dangantakar da ke tsakaninsu. Tana kuma bayyana wa duk duniya cewa, kasar Sin wadda ke neman samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, kuma ke kokarin raya wata kasa mai jituwa cikin lumana muhimmin karfi ne wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duk duniya. Ko shakka babu, al'ummomin Sin za su taka sabuwar rawa wajen ciyar da wayin kan dan Adam gaba. (Sanusi Chen)