Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-11 17:07:42    
Hadin gwiwa tsakanin kasashen Seychelles da Sin ya taka wani sabon mataki

cri
A ran 10 ga wata, shugaban kasar Seychelles James Alix Michel ya bayar da sanarwa a birnin Victoria, babban birnin kasar, cewa ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi a kasar Seychelles wani babban batu ne wajen bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wadda ta shaida cewa, hadin kai tsakanin kasashen biyu ya bude wani sabon shafi.

Lokacin da shugaba Hu ke cikin shirin bar kasar Seychelles, shugaba Michel ya bayar da sanarwa ga kafofin watsa labarai a filin jirgin sama, inda ya taya murna ga shugaba Hu da ya samu kyakkyawar nasara wajen ziyararsa a kasar Seychelles, kuma ya nuna yabo kan ci gaban da aka samu daga dukkan fannoni a cikin wadannan shekaru 30 da suka wuce bayan da kasashen Seychelles da Sin suka kulla huldar diplomasiyya. Ban da wannan kuma ya bayyana cewa, ko da yake ana kasancewar bambanci tsakanin kasashen biyu wajen tattalin arziki da tsarin al'umma da kuma fadin yankunan kasa, amma bangarorin biyu suna da ra'ayin bai daya wajen al'amuran nan gaba da bunkasuwa da kuma zumunci.

Bugu da kari kuma shugaba Michel ya ce, lokacin da kasar Seychelles ke yin kokari wajen samun dauwammaniyar ci gaban tattalin arzikin kasar, kasar Sin ta kara zuba jari ga Seychelles, shi ya sa Seychelles ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiya mafi muhimmanci wajen samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.(Kande Gao)