Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-11 17:06:56    
Hu Jintao ya dawo nan birnin Beijing bayan da ya gama ziyara a kasashen Afirka 8

cri
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya dawo nan birnin Beijing ta jirgin sama na musamman a ran 11 ga wata da safe bayan da ya gama ziyarar aiki a kasashen Afirka 8. Kuma matarsa Liu Yongqing, da wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin Tang Jiaxuan da sauran 'yan rakiyarsa sun iso Beijing tare.

A ran 10 ga wata, ministsan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana cewa, wannan ziyarar da shugaba Hu ya yi a kasashen Afirka 8 wata ziyara ce wajen sada zumunci da hadin kai tare da dukkan kasashen Afirka, kuma ita wani muhimmin batu daban ne na dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka bayan da aka kira taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wadda za ta taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka a nan gaba. Haka kuma an shaida cewa, kasar Sin wadda ke bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da raya kasa mai jituwa, da kuma samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya wani muhimmin karfi ne wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a duk duniya, kuma kasar Sin za ta bayar da sabuwar muhimmiyar gudummowa ga ci gaban wayin kan dan Adam.(Kande Gao)