Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-10 18:42:37    
Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya fara ziyarar aiki a kasar Seychelles

cri

Bisa gayyatar da Mr James Alix Michel, shugaban Jamhuriyar Seychelles ya yi masa ne, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya sauka birnin Victoria, hedkwatar kasar don fara yin ziyarar aiki.

Ziyarar da shugaba Hu Jintao ke yi a kasar Seychelles, ziyarar farko ce da shugaban kasar Sin ke yi a kasar, kuma karo na farko ne kasar Seychelles ta karbi shugaban kasar waje a cikin kimanin shekaru 20 da suka wuce. Gwamnatin kasar da jama'arta suna nuna girmamawa sosai ga shugaba Hu Jintao da 'yan kungiyarsa.

Mr Michel, shugaban kasar Seychelles ya je filin jirgin sama don tarye shugaba Hu da kungiyarsa, inda ya shirya gaggarumin bikin maraba da zuwansu. A lokacin tashin kida mai dadin ji, shugaba Hu Jintao ya duba farati da aka shirya masa.

A daidai wannan lokaci, gidan rediyon kasar Ceychelles yana watsa wakoki na kasar Sin. Da baki na kasar Sin wadanda suka fito daga nisa sun ji wakokin, sai sun ji kamar komawa gida ke nan, kuma sun fahimci sosai cewa, idan akwai aboki nagari kome nisansa, tamkar kusa yake.

A filin jirgin saman, Mr Hu Jitao ya bayar da jawabi a rubuce cewa, a cikin shekaru 30 da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasashen Sin da Seychelles, sun girmama wa juna, sun yi zama tare cikin daidaici, sun yi ta samun sabon ci gaba wajen hadin kansu a fannoni daban daban, kuma sun yi ta yin shawarwari da tattaunawa a kan harkokin duniya. Ya yi imani cewa, tabbas ne, ziyararsa za ta kara dankon amincin gargajiya a tsakanin kasashen biyu, da kara inganta hadin kansu na sada zumunta, da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.

Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasashen Sin da Seychelles a shekarar 1976, an yi ta samu ci gaba wajen yin hadin guiwar tattalin arziki da fasaha a tsakanin kasashen biyu, da kara yin ma'amalar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu. Kasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin hadin guiwa a tsakaninsu a fannin tattalin arziki da fasaha da aikin su da sauransu. Manyan kayayyaki da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Seychelles sun hada da na'urori da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki da kayayyakin alatu na gida da tufafi da kayayyakin roba da sauransu, sa'an nan kuma manyan abubuwa da kasar Sin ke shigowa daga kasar Seychelles su ne albarkatun teku. Yawan kudi da aka samu daga wajen ciniki a tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka miliyan 5 da dubu 470 a tsakanin watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar bara.

A cikin bayaninta, wakiliyarmu Zhang Hui ta bayyana cewa, cikin nuna babbar gwaninta, ma'aikatan wasu kamfanonin gine-gine na kasar Sin suka yi ayyukan gine-gine masu yawa a kasar Seychelles a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ta haka gwamnatin kasar Seychelles sun nuna babban yabo gare su. Ta kara da cewa, manyan ayyukan gine-gine da kamfanonin kasar Sin suka sami kwangilarsu sun hada da makarantu da gine-ginen ofisoshi a kasar Seychelles. Alal misali, babban gini wanda babban kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina domin hukumar kula da harkokin ma'auni ta kasar Seychelles, ya riga ya zama kyakkyawan misali ga aikin gine-gine na kasar. Ya zuwa watan Nuwamba na shekarar bara, jimlar kudi da kasar Sin ta samu bisa kwangilar da ta samu ta kai dalar Amurka miliyan 273 a kasar Seychelles." (Halilu)