Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-09 21:09:44    
Ziyarar shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao a Mozambique

cri

Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya isa birnin Maputo hedkwatar kasar Mozambique a Jiya Alhamis domin yin ziyarar aiki bisa gayyatar da shugaba Armando Guebuza na wannan kasa ya yi masa. To, yanzu ga wani labarin da wakiliyarmu ta ruwaito mana.

Kasar Mozambique tana kudu maso gabashin nahiyar Afrika kuma tana kusa da tekun India. Tuni kafin a samu 'yancin kasar Mozambique, sai gwamnatin kasar Sin ta sanya matukar karfi wajen goyon bayan gwagwarmaya da kungiyar 'yantar da Mozambique ke yi don samun mulkin kan al'ummar kasar. Lallai ba a manta ba, a ran 25 ga watan Yuni na shekarar 1975 wato daidai ranar da kasar Mozambique ta samu 'yancin kai, kasashen biyu wato Sin da Mozambique sun kulla huldar jakadanci tsakaninsu. A cikin shekaru sama da 30 da suka shige, jama'ar kasashen biyu sun kulla aminci mai zurfi tsakaninsu. Ziyarar Mr. Hu Jintao a wannan gami, ziyara ce ta farko da shugaban kasar Sin ya kai wa kasar Mozambique, inda ya samu kyakkyawar maraba daga gwamnatin Mozambique da jama'arta.

Shugaba Guebuza na Mozambique shi kansa ne ya je filin jirgin sama don taryen shugaba Hu Jintao da 'yan kungiyarsa, inda aka gudanar da gagarumin bikin duba faratin girmamawa.

Dubban mutane sanye da kyawawan tufafi na Mozambique sun yi raye-raye da wake-wake cikin halin annashuwa don yin lale marhabin da shugaba Hu Jintao da 'yan rakiyarsa.

Jama'a masu sauraro, mun san cewa, kasar Mozambique tana daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya. Tun cikin dogon lokaci ne, gwamnatin kasar Sin ta ta tallafa mata ta hanyoyi daban daban gwargwadon iyawa.

Saukar shugaba Hu Jintao ke da wuya, sai nan da nan ya yi shawarwari tare da takwaransa Mr. Guebuza na Mozambique. Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa guda takwas a fannin tattalin arziki da cinikayya, da noma, da ilimantarwa da kuma na wasannin motsa jiki da dai sauran fannoni, inda Mr. Hu Jintao ya fadi, cewa

' Na zo nan Mozambiqe ne domin aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing wato dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika, da inganta zumuncin gargajiya na kasashen biyu, da kara yin hadin gwiwa ta hakika da kuma samun bunkasuwa tare. Dazu, na yi shawarwari tare da shugaba Guebuza cikin halin aminci, inda muka samu ra'ayi iri daya kan yadda za a kara inganta kyakkyawar huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Ban da wannan kuma, dukaninmu mun yarda da rika yin mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu ,da karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, da yin musanye-musanye a fannin zamantakewar al'adu, da kuma kara daidaituwa da kasashen biyu suke yi game da lamuran kasa da kasa. Jerin takardun da aka rattaba hannu a kai, lallai sun zama tamkar shaida ce ta hakika ta habakawar hadin gwiwa da ake yi tsakanin kasashen biyu.'

Sa'annan shugaba Hu jintao ya shelanta, cewa domin aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing da kuma tallafa wa kasar Mozambique wajen bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar jama'arkasar, bangaren kasar Sin ya tsaida kudurin ci gaba da bayar da gudummuwa ga Mozambique a fannin soke biyan rancen kudi da bangaren Mozambique ya samu daga gwamnatin kasar Sin ba tare da samun riba ba da kuma kara yawan ire-iren hajjoji da bangaren Mozambique yake sayar wa kasar Sin ba tare da biyan kudin kwastan ko kwabo ba da dai sauran fannoni.

A nasa bangare, shugaba Guebuza ya yi farin ciki da fadin cewa,

' Ziyarar da shugaba Hu Jintao yake yi a wannan gami ta kasance tamkar akiba ce da aka samu sakamakon kasancewar zumunci mai zurfi a tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. Kasar Sin ta bai wa kasar Mozambique gudummuwa ta hanyoyi da dama kuma ba tare da son rai ba. Mun yi musanye-musanyen ra'ayoyi sosai kan halin da ake ciki yanzu a duniya. Mun kuma yi hasashen cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya, wani sharadi ne da ba za a iya rasa shi ba na yalwata zamantakewar al'ummar kasa da kasa da kuma na kawo zaman alheri ga jama'ar kasashen duniya. ( Sani Wang )