Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-09 18:36:09    
Kasar Sin tana bunkasa harkokin tattalin arziki mai zaman kansa cikin sauri

cri
Bisa sabon sakamakon bincike da aka samu, an ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta bunkasa harkokin tattalin arziki mai zaman kansa cikin sauri. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan masana'antu masu zaman kansu ya riga ya wuce miliyan 4 da dubu 900 a kasar Sin. Yanzu, ba ma kawai masana'antun suna gudanar da harkokinsu a fannin tattalin arzikin yau da kullum kamar saka da yin tufafi da gyara amfanin gona da sayar da kayayyaki da sauransu ba, har ma suna yin harkokinsu a fannin tattalin arziki mai muhimmanci kamar samar da kwal da gas da ruwa da ayyukan jin dadin jama'a da aikin kudi da sauransu, sa'an nan gurabe da sharuda da suka samu wajen gudanar da harkokinsu sun yi ta samun kyautatuwa.

A gun taron manema labaru da aka shirya a ran 9 ga wata, Malam Bao Yujun, shugaban kungiyar binciken harkokin tattalin arziki mai zaman kansa ta kasar Sin ya gabatar da rahoto kan binciken masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin cewa, "a cikin shekarun nan biyu da suka gabata, yawan masana'antu masu zaman kansu ya karu cikin sauri a kasar Sin. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawansu ya wuce miliyan 4 da dubu 900, masu gidan masana'antun da ma'aikata da suka dauka sun riga sun wuce miliyan 130. Bisa kidayar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan mutanen birane da garuruwa na kasar Sin wadanda ke da aikin yi ya kai miliyan 273 a shekarar bara, wato ke nan yawan masu masana'antun da ma'aikata da suka dauka ya dauki rabin yawan mutanen nan masu aikin yi."

Daga binciken da aka yi, an gano cewa, a cikin shekarun nan da suka wuce, an bunkasa masana'antu masu zaman kansu kamar yadda ya kamata a kasar Sin, alal misali, don ta masana'antu masu zaman kansu wadanda suka shafe shekaru biyar suna gudanar da harkokinsu, kwatakwacin kudin jari da suke samu ya yi ta karu da kashi 15 cikin dari a ko wace shekara. Masana'antun nan wadanda ke samun kudin Sin Renminbi Yuan sama da miliyan 10 daga wajen sayar da kayayyakinsu a ko wace shekara sun karu sosai, idan an kwatanta su da na shekarun baya.

Bisa binciken da aka yi, an ce, a halin yanzu, gurabe da sharuda da ake samar don aiwatar da harkokin tattalin arziki mai zaman kansa ya sami kyautatuwa a zahiri a kasar Sin, idan an kwatanta su da na shekarun baya. Gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofi da dama don sa kaimi ga bunkasa masana'antu masu zaman kansu da ba su jagoranci da taimako, kuma ta yarda da su gudanar da harkokinsu a fannin hanyoyin jiragen kasa da sadarwa da zirga-zirgar jiragen saman fasinja da aikin kudi da sauransu. Ka zalika misalin kashi 10 cikin dari na masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin sun kulla huldar hadin kan kudin jari tare da masana'antun kasashen ketare, wasunsu kuma sun riga sun zuba jari don kafa masana'antu a kasashen waje.

Amma, yanzu yana kasancewa da matsaloli da wahalhalu, yayin da ake bunkasa masana'antu masu zaman kansu a kasar Sin. Malam Bao Yujun, shugaban kungiyar nazarin harkokin tattalin arziki mai zaman kansa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "daga binciken da aka yi a wannan gami, an gano cewa, an canja ka'idoji masu wahala da masana'antu masu zaman kansu ke fuskanta wajen neman rancen kudi. Yau da shekaru biyu da suka wuce, manyan ka'idojin su ne abubuwa masu sarkakiya da su kan yi wajen samun rancen kudi, amma yanzu, sharudan jingina da wanda zai tsayawa mai neman rancen kudi sun kara tsananta. Yawancin masana'antun sun bayyana cewa, kudi da suke kashewa wajen samun rancen kudi ya yi yawa."

Dangane da wahalar da masana'antu masu zaman kansu ke sha wajen samun rancen kudi, gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki matakai wajen rage yawan kudi da suke kashewa wajen samun rancen kudi. Masana'antu masu zaman kansu su ma suna fatan za su yi kara yin ma'amala da hukumomin gwamnati don kara kyautata gurabensu na samar da kayayyaki ta yadda za su kara samun bunkasa cikin sauri kuma yadda ya kamata. (Halilu)