Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-09 16:13:24    
An soma gudanar da yunkurin ' Hadin gwiwa na zuciya da zuciiya 'domin ba da ilmi game da wasannin Olympic

cri

Jama'a makaunata, kwanakin baya ba da dadewa ba, a nan birnin Beijing, an gudanar da yunkurin ' Hadin gwiwa na zuciya da zuciya' domin bada ilmi game da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 daidai a ranar cika kwanaki 600 da suka yi saura ga yin bikin bude gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

A gun bikin gudanar da yunkurin a jami'ar Jama'a ta kasar Sin, Mr. Liu Qi, sakataren kwamitin birnin Beijing na kwamtin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, da malam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin kuma mataimakiyar shugaba na farko na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun taba wani kwallo mai launuka iri biyar tare, nan take 'yan makarantun midil da na firamare suka yi kuwwa cikin farin ciki. Bisa irin wannan kyakkyawan hali ne, aka soma gudanar da yunkurin ' hadin gwiwa na zuciya da zuciya'.

Madam Chen Xiaoya, mataimakiyar ministan ilimantarwa na kasar Sin ta bayyana yadda aka tsara shirin ' hadin gwiwa na zuciya da zuciya'. Ta furta cewa, domin yin lale marhabin da gagarumin taron wasannin Olympic da za a gudanar da shi a nan Beijing a shekarar 2008, kuma domin barin samari matasa na kasar Sin da na sauran kasashen duniya su tabbatar da kyakkyawan burin Olympic na " hadin kai, da zumunci da kuma zaman lafiya", ma'aikatar ilmantarwa ta kasar Sin da kuma kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun karbi shawarwarin da abun ya shafa daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa wato na kaddamar da shirin bada ilmi game da wasannin Olympic cikin hadin gwiwa ,wanda kuma ke da sigar musamman ta kasar Sin.

Daga baya dai, Madam Chen Xiaoya ta bayyana cewa, yara na birnin Beijing sun lakaba wa wannan harka dake da sigar mumsamman ta al'adun gargajiya na kasar Sin a kan cewa ' Shirin Zuciya da zuciya', wanda ya alamanta, cewa a karkashin tuta mai zobba biyar na Olympic, samari da yara na kasashe da na jihohi daban daban na duniya suna kokarin cimma kyakkyawan burinsu na raya wata duniya mai jituwa cikin hannu da hannu kuma zuriya da zuriya.

An tanadi hakikanan abubuwa a cikin wannan shiri kamar haka: makarantun sakandare da na firamare fiye da 200 na birnin Beijing wadanda suke halartar harkar nan za su yi cudanya tare da kwamitocin wasannin Olympic da kuma kwamitocin wasannin Olympic na nakasassu na kasashe da jihohi daban daban, kuma za su yi cudanya da wata makaranta ta wata kasa ko wata jiha don kulla huldojin abokantaka. Bisa shirye-shiryen da aka tsara, a nce, kafin a bude taron wasannin Olympic, daliban makarantun da suka kulla huldojin abokantaka tsakaninsu za su yi koyo da kuma samun ilmi game da harshe, da al'adu ,da tarihi, da labarin kasa, da halayen gargajiya da kuma bukukuwan nuna adabi na kowanensu da yin musanye-musanye tsakaninsu; Ban da wannan kuma, wakilan dalibai da na malamai na makarantun da suka kulla huldojin abokantaka za su halarci bikin maraba a kauyen Olympic da kuma sa kaimi ga kungiyoyin wakilai ta wasannin motsa jiki na kasashe da jihohi wadanda suka kulla huldojin abokantaka tsakaninsu a gun gasanni, har da gayyatar 'yan wasa zuwa makarantun domin yin ziyara da yin nishadi.

Makasudin kaddamar da shirin " Hadin gwiwa na zuciya da zuciya", shi ne don daukaka ci gaban musanye-musanye tsakanin 'yan makarantun midil da na firamare na birnin Beijing da samari matasa na wurare, inda 'yan babban iyalin Olympic ke zaune; haka kuma don yin namijin kolari wajen tabbatar da aniyar " Duniya daya kuma kyakkyawan buri daya", ta yadda za a samo hasashen Olympic tare na " Hadin kai, da zumunci da kuma zaman lafiya". Wannan harkar da ake gudanarwa ta samu goyon baya daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa.

A karshe dai, Madam Chen Xiaoya ta hakkake, cewa harkar nan ta " Hadin gwiwa na zuciya da zuciya" za ta kago wani irin kyakkyawan muhallin zamantakewar al'adu ga taron wasannin Olympic na Beijing da kuma kyakkyawan halin zumunci na yin lale harhabin da 'yan wasa na kasashe da jihohi daban aban na duniya.( Sani Wang )