Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-09 09:56:40    
Kasashen Sin da Mozambique sun bayar da sanarwar hadin gwiwa

cri

A ran 8 ga wata, a birnin Mapulo, hedkwatar kasar Mozambique, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Mozambique ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, za su aiwatar da ra'ayin bai daya da suka samu domin inganta dangantakar hadin gwiwa ta aminci tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki da kuma amfana wa jama'ar kasashen biyu.

A cikin shawarwarin, shugaba Hu ya bayar da shawarwari hudu wajen ciyar da dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin kasashen Sin da Mozambique gaba, wato za a kara yin cudanya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu don kara amincewar juna a fannin siyasa, da taimaka wa juna don karfafa hadin kansu wajen tattalin arziki da cinikayya, da inganta mu'amalar da ke tsakaninsu a fannin al'adu, ta yadda za a iya kara karfin tushen zamantakewar al'umma wajen hadin kai da aminci, da kuma kara hadin gwiwarsu a cikin harkokin kasashen duniya domin kiyaye moriyar bai daya. Haka kuma shugaba Guebuza ya bayyana cewa, bangaren Mozambique yana fatan kara yin cudanya tare da bangaren Sin domin koyi da sakamako mai kyau da Sin ta samu.

Ban da wannan kuma a ranar, kasashen Sin da Mozambique sun bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda bangarorin biyu suka amince da kara yin cudanya tsakanin gwamnatoci da majalisun dokoki na kasashen biyu da kuma tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma Jam'iyyar 'yantar da kasar Mozambique, da kara hadin kansu wajen tattalin arziki da cinikayya don moriyar juna, da inganta yin mu'amala tsakaninsu a fannonin zamantakewar al'umma da al'adu, ta yadda za a iya karfafa da kuma bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.(Kande Gao)