Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-08 21:24:36    
(Sabunta) Shugabannin Sin da Mozambique sun yi shawarwari

cri
Ran 8 ga wata da dare agogon Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin, wanda ya isa birnin Maputo na kasar Mozambique, don yin ziyarar aiki a kasar, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Mr. Armando Emilio Guebuza, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimman batutuwan shiyya-shiyya da na duniya.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu za su halarci bikin sa hannu kan takardun hadin kai a jere a tsakanin bangarorin biyu, kuma za su gana da manema labaru tare.

Bayan da ya isa filin jirgin sama, shugaba Hu ya bayar da wani jawabi a rubuce cewa, a cikin shekaru 31 da suka gabata tun bayan da kasashen Sin da Mozambique suka kafa dangantakar diplomasiyya, kasashen biyu suna kara raya dangantakarsu sosai da sosai. Kasar Mozambique ta zama kyakkyawar kawa ta kasar Sin.

Mr Hu ya ce, makasudin ziyararsa a kasar Mozambique shi ne domin kara karfafa zumuncin gargajiya a tsakanin bangarorin biyu, kuma da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, da kuma tsara shirin bunkasa dangantakarsu da kara hadin kansu a nan gaba. (Bilkisu)