A ran 8 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Maputo domin fara ziyarar aiki a kasar Mozambique bisa gayyatar da takwaransa na kasar Armando Emlio Guebuza ya yi masa.
Mr Guebuza ya shirya gaggarumin bikin a filin jirgin sama domin maraba da ziyarar shugaba Hu.
Bayan da ya isa filin jirgin sama, shugaba Hu ya bayar da wani jawabi a rubuce cewa, a cikin shekaru 31 da suka gabata tun bayan da kasashen Sin da Mozambique suka kafa dangantakar diplomasiyya, kasashen biyu suna kara raya dangantakarsu sosai da sosai. Kasar Mozambique ta zama kyakkyawar kawa ta kasar Sin.
Mr Hu ya ce, makasudin ziyararsa a kasar Mozambique shi ne domin kara karfafa zumuncin gargajiya a tsakanin bangarorin biyu, kuma da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, da kuma tsara shirin bunkasa dangantakarsu da kara hadin kansu a nan gaba.(Danladi)
|