Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bar birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu a ran 8 ga wata da safe agogon wurin, bayan da ya kawo karshen ziyarar aiki a kasar, kuma ya nufi kasar Mozambiqu, domin ci gaba da ziyararsa a kasashe 8 na Afrika.
A lokacin ziyararsa, shugaba Hu jintao ya yi musayen ra'ayoyi sosai tare da Mr. Thabo Mvuyelwa Mbeki, takwaransa na kasar Afrika ta kudu, da kuma sauran kusoshin kasar kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu duka, kuma sun samu ra'ayi daya a fannoni daban daban. Bayan haka kuma ya yi jawabi a Jami'ar Pretoria ga samarin PAN Afrika, inda ya jaddada cewa, ya kamata a kara dankon aminci a tsakanin Sin da Afrika daga zuriya zuwa zuriya don sa kaimi ga raya duniya mai jituwa. Bayan haka kuma shugaba Hu Jintao ya kai ziyara a kufan mafarin dan 'Adan.
Kasar Afrika ta kudu ita ce ta 6 a cikin jeren kasash 8 na Afrika da shugaba Hu yake ziyarar aiki a wannan gami. Kafin wannan, ya kai ziyara ga kasashen Cameroon, da Liberiya, da Sudan, da Zambia, da kuma Namibia. Kuma zai kai ziyara a kasashen Mozambique, da Seychelles. (Bilkisu)
|