Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-08 16:16:05    
Kasar Sin da Afirka sun samu ci gaba tare wajen wayewar kansu

cri
A ran 7 ga wata, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki a Afirka ta kudu ya kai ziyara a tsohon wurin tarihin dan adam na Maropeng wanda aka shigar da shi cikin sunayen kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na duniya, kuma ya sanar da cewa gwamnatin sin za ta ba wa asusun kayayyakin tarihin Afirka taimakon kudin dala miliyan daya domin bayyana babban zumuncin da jama'ar sin ke nuna wa jama'ar Afirka, sa'an nan kuma domin nuna goyon baya ga ayyukan da Afirka ke yi wajen kiyaye kayayyakin tarihi na duniya. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayanin da wakilanmu na musamman suka ruwaito mana wanda yake da lakabi haka "Kasar Sin da Afirka sun samu ci gaba tare wajen wayewar kansu, wato bayani game da gwamnatin kasar Sin ta ba da kyautan kudi domin kiyaye kayayyakin tarihi na duniya da ke Afirka.

Tsohon wurin tarihin dan adam wanda fadinsa ya kai kadada dubu 50 yana cikin wani kwarin dutsen da ke yammacin birnin Johannesburg, birnin mafi girma na kasar Afirka ta kudu. Shi ne kogunan Sterkfontein Caves wanda yake hade da wurane masu ni'ima fiye da 300.

Mr. Mbhazima Shilowa, shugaban lardin Gauteng inda kayayyakin tarihi suke ya bayyana cewa, kalmar Maropeng ma'anarta ita ce mafarin wayewar dan adam, a shekarar 1999, hukumar Unesco ta M.D.D. ta shiga da wannan wuri cikin sunayen kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na duniya domin kiyaye kayayyakin tahiri da aka gano a nan. Ya ce, "Wannan tsohon wurin kayayyakin tarihi ya tabbatar da cewa mafarin dan adam yana Afirka.Bayan shigar da tsohon wurin dan adam na mutanen Beijing cikin wadannan sunaye, kafin shekaru 12, sai aka shigar da tsohon wurin tarihin dan adam na Maropeng cikin sunayen kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na duniya"

Mr. Shilowa ya bayyana cewa, yanzu a duniya an sha bamban tsakanin mutane masu launin fata daban-daban wajen al'adu da bin addini, amma dukkansu mutune ne wadanda suke da dogon tarihi iri daya. Ko da yake aminanmu Sinawa sun zo ne daga wancen gafe na duniya, amma "iyalinmu daya ne".

Bayan da Mr. Hu Jintao ya karasa ziyararsa a tsohon wurin kayayyakin tarihin dan adam na Maropeng, ya bayyana cewa, kayayyakin tarihi masu daraja da ke wannan tsohon wuri sun kara tabbatar da cewa, Afirka mafarin wayewar dan adam ne, kuma Afirka ta ba da fiffitaccen taimako ga ci gaban dan adam. Ya kuma bayyana cewa, domin nuna goyon baya ga sha'anin kiyaye al'adun Afirka, kuma domin bayyana babban zumuncin da jama'ar Sin ke nuna wa jama'ar Afirka ta kudu, gwamnatin kasar Sin ta yanke kuduri cewa, za ta ba da kyautan kudi na dala miliyan daya ga asusun kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na duniya da ke Afirka. Ya ce, "Muna fatan da zuciya daya ga masu binciken kayayyakin tarihi na kasashen 2 wato Sin da Afirka ta kudu za su kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma su kara ba da babban taimako wajen tono asirin kayayyakin tarihi na dan adam. Na hakkake cewa, bisa matsayin taimakon juna da samun wadata tare tsakanin wayewar kasar Sin da ta Afirka wadanda suke su ne kayayyakin tarihi masu daraja sosai na dan adam, ba shakka za su kara ba da babban taimako ga sha'anin ci gaban zaman lafiya da samun bunkasuwar dam adam."

A gun bikin ba da kyautar kudin da aka yi a wannan rana, Mr. Pallo Jordan, ministan fasaha da al'adu na kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, tun bayan da aka kulla dangantakar diplomasiya tsakanin Afirka ta kudu a ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1998 zuwa yanzu, dangantakar samun moriyar juna da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2 kullum tana ta samun ci gaba lami lafiya. Ya ce, "Kayayyakin tarihi da al'adu da fasaha sun ba da taimako na musamman domin samun jituwar zaman al'umma. Sabo da haka aikin kiyaye tsoffin wuraren kayayyakin tarihi na duniya kamar na nan Maropeng, ba ma kawai yana da muhimmanci ga Afirka ta kudu ba, har ma ga sauran kasashen duniya." (Umaru)