Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 21:52:33    
Kanllon kankara da kuma yin wasa da kankara mai taushi a birnin kankara

cri

Birnin Harbin na cikin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, an kira shi 'birnin kankara', saboda matsassakaicin yawan sanyi yi kasa da digiri sifiri har tsawon watanni 5 a ko wace shekara. Sanyi ya kawo wa 'yan birnin basira, a lokacin hunturu sun yi wa birnin Harbin ado da kankara da kankara mai taushi, har ma Harbin ta zama wani kyakkyawan wuri ne da aka iya gani a cikin hikaya kawai.

Birnin Harbin yana yankin kusurwar sama a doron kasa, yawan sanyi ya yi kasa da digiri sama da 20 a karkashin sifiri a farkon lokacin hunturu. Sanyi ya karfafa kyan ganin Harbin sosai, Harbin kuwa ta samar da al'adunta na musamman mai launin fari, ta shirya bikin al'adu na kankara da kankara mai taushi, wato bikin kankara da kankara mai taushi na duniya. Tun daga shekara ta 1985 da ta gabata, wannan kasaitaccen biki ya kan karbi baki daga wurare daban daban a ko wace ranar 5 ga watan Janairu.

An yi kwanaki sama da 100 ana yin wannan bikin kankara da kankara mai taushi. A lokacin nan, mutum-mutumin da aka yi da kankara sun tsaya a tituna da unguwoyin Harbin. Ba da nufi ne mutane su kan ga biyanon da aka yi da kankara da alamun nuna fatan alheri na taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 wato Fuwa. Ban da wannan kuma, mutane su kan sa kayayyakin launuka ko kuma fitilu masu launuka a cikin bayanannen kankara, ta haka mutum-mutumin da aka yi da kankara na da bayananne, kuma suna yin haske masu launuka iri daban daban da dare.

Yanzu za mu gaya muku yadda aka sassaka wadannan mutum-mutumi da kankara. Bayan da lokacin hunturu ya yi, kogin Songhuajiang da ke kewayen birnin Harbin ya zama wani babban fili mai kankara, har ma idan kankara na da zurfi, mota na iya gudu a kansa. 'Yan birnin Harbin masu fasaha sun haka kankara, sun yi amfani da injin yanka na musamman sun yayyanka kankara zuwa siffofi daban daban, daga baya, sun sassaka mutum-mutumi da wadannan kankara.

Idan ba ku gamsu da mutum-mutumin da ke kan tituna da wuraren shakatawa ba, to, wurin shakatawa da ke gabar arewa ta kogin Songhuajiang wuri ne da ke biyan bukatunku. Fadinsa ya kai murabba'in mita 400,000 ko fiye, wanda wurin shakatawa ne mafi girma a birnin Harbin, inda aka nuna kayayyakin kankara da kankara mai taushi. A cikin wannan wurin shakatawa, hasumiyoyi da dakuna da fada da kuma manyan fada dukansu aka yi su da kankara. Mutane na iya sa kafa kan benayen kankara a maimakon kallonsu kawai.

Ban da mutum-mutumin da aka yi da kankara, an sassaka mutum-mutumi da kankara mai taushi a Harbin. Tsibiri mai suna Taiyangdao da ke arewacin gabar kogin Songhuajian wuri ne mai kyau wajen kallon mutum-mutumin da aka yi da kankara mai taushi. Saboda iska na da tsabta, kuma kankara mai taushi na da kyau a nan, shi ya sa hukumar Harbin ta kan shirya bikin baje-koli na mutum-mutumin da aka yi da kankara mai taushi sau daya a ko wace shekara.

'Yan birnin Harbin ba su yi kayayyakin fasaha da kankara da kankara mai taushi kawai ba, har ma sun gina na'urorin shakatawa da su. A cikin wurin shakatawa na Zhaolin na Harbin, an gina wata babbar hanyar fita daga daki mai wahalar ganewa da kankara, wadda tsawonta ya kai misalin mita 60, tilas ne mutane su mai da hankali sosai, kada santsi ya kwashe su a lokacin da suke neman fita waje a cikin wannan babbar hanyar fita daga daki mai wahalar ganewa. Sa'an nan kuma, kada su manta da yin wasa da sululu mai tsawon mita 10 ko fiye. A lokacin da wani ya gangaro daga kansa cikin sauri kan hanyar kankara, sai a ji iska ta buga a bakin kunnensa, ba a iya kwanta da zuciya ba.

Idan kana son kara jin dadin wasannin kan kankara, to, tabbas ne ka je kogin Songhuajiang. Bayan da ruwan kogin ya daskare, kogin Songhuajiang ya zama wurin shakatawa ne na halitta a birnin Harbin. Mutane na iya kallon wurare masu ni'ima da ke gabobin kogin kan kekunan tafiya da karnuka suka ja a kan kankara, haka zalika kuma suna iya kallon masu kishin iyo a lokacin hunturu na iyo a cikin kogin.

In an tabo magana kan wasannin kan kankara, tilas ne mu tuna da wasan skiing a tsakanin duwatsu. Birnin Harbin wuri ne mai dacewa da wannan wasa. A cikin dukan filayen wasan skiing a tsakanin duwatsu da ke wannan birni, filin wasan skiing a tsakanin duwatsu na Yabuli ya fi shahara, wanda ya fi girma a duk kasar Sin. Yana kan gaba a kasar Sin a fannonin yawan hanyoyin wasan skiing da aka shimfida da kuma tsawonsu da tsayinsu da kuma samar da sauran na'urorin wasan skiing.(Tasallah)