Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 21:51:42    
Sharhin masu sauraro a kan ziyarar shugaban kasar Sin a kasashen Afirka guda takwas

cri

Tun daga ranar 30 ga watan jiya har zuwa ranar 10 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya kai ziyarar sada zumunta da hadin gwiwa a kasashe takwas na nahiyar Afirka, wato su ne Kamaru da Liberia da Sudan da Zambia da Namibia da Afirka ta kudu da Mozambique da kuma Seychelles, kuma bayan da muka bayar da labarin wannan ziyara, sai bi da bi ne muka sami wasu sakonni daga masu sauraronmu, inda suka ba mu sharhinsu a kan ziyarar.

Malam Bala Mohammed Mando wanda ya fito daga MAITAMA DISTRICT, ABUJA, NIGERIA, ya rubuto mana cewa, ina mai cikakken farin ciki a kan ziyarar da shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya fara a kasashen Afirka takwas wanda ita ce ziyararsa ta farko a wanna shekarar. Kuma wannan dankon zumunta da Shugaba Hu Jintao yake sakawa a tsakanin Sin da Afirka abu ne wanda ya zo a dai-dai lokacin da Afirka ta ke bukatar muhimmiyar madogara ta fannoni daban-daban domin bunkasa al'amuranta da kuma matsayarta a siyasar duniya. Mu mutanen Afirka muna sa ran Shugaba Hu Jintao zai yi amfani da wannan dama ta ziyarar da yake yi domin tattaunawa da shugabannin gwamnati, manya da kananan 'yan kasuwa, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin malamai, shugabannin dalibai, da kungiyoyin sa kai da kuma na kare hakkin dan adam, tare da 'yan jarida. Muna kuma sa ran cewa kasar Sin za ta ci gaba da nuna irin wannan kauna da take yi ga nahiyar Afirka, wanda shi ne ya sa jama'ar nahiyar suke kara yin na'am da manufofin kasar Sin a kan Afirka.

Bayan haka, ina so in yi bayani ne akan rahotannin wasu jaridun Afirka a kan dangantakar Sin da Afrika.

"Akwai tsoro a zukatan wadansu 'yan Afirka a kan cewa kasashen Afirka masu raunin tattalin arziki za su iya yin babbar hasara daga fadada hanyoyin kasuwanci da ciniki da Sin, in har ba su yi cikakken nazarin yarjejeniyar dangantakar kasa-da-kasa tsakaninsu da Sin ba. Sannan kuma in ba su kare kananan masana'antunsu ba daga kayayyakin kamfanonin Sin masu araha."

A dangane da bayanin nan na sama, ziyarar Shugaba Hu Jintao za ta iya zama wata kafa ta wayar da kan al'ummar Afirka, domin su gane cewa manufofin Sin a kan Nahiyar Afirka ya wuce yadda wasu suke zato. Musamman ma idan aka tuna ziyarar da Hu Jintao ya yi zuwa Afirka a baya, sun kawo yafe basussukan da kasar Sin ke bin wasu kasashen Afirka, da kuma alkawuran gina asibitoci, madatsun ruwa da kuma filayen wasa da sauransu. Kuma za a iya tunawa a taron koli da aka yi na Sin da Afirka a Beijing a watan Nuwamba na shekarar 2006, Mr.Hu Jintao ya yi tayin ba da bashin Dola biliyan biyar ga wasu kasashen Afirka, kuma ya yi alkawarin rubanya gudummuwa, kuma ya tabbatar da cewa, dangantakar Sin da Afirka ya wuce kwadayin mamaye al'amuran kasuwanci, da kuma kwadayin samu da kuma sarrafa man fetur da Afirka ke samarwa.

A karshe kuma dangantakar Sin da Afirka Alheri ne a gare mu domin akwai dimbin abubuwan alheri da Afirka za ta karu da su a dangantaka da Sin.

Bayan haka, a cikin wasikar da malam Mamane Ada mazaunin birnin Yamai, jamhuriyar Nijer ya aiko mana, ya ce, wannan ziyara ta mai girma shugaban kasar Sin Hu Jintao cikin wadannan kasashe takwas na Afirka, wannan ba ita ce ta farko ba, amma ga wannan karo, tafiyar shugaban Sin na da tasiri babba ganin cewa rangadin ya kumshi kasa takwas. Hakika zamantakewar bangarorin biyu ta zo daidai da zaman manomi da makiyayi. Wannan rangadi na shugaba Hu Jintao cikin wadannan kasashe 8 da kuma kara nuna bukata ta ido da ido na tabbatar da cigaban Afirka. Daga karshe, ana kyautata zaton cewa, wata rana sai kasar Nijar ta karbi bakuntakar shugaba Hu Jintao.

Sai kuma malam Salisu Muhammed Dawanau, mazaunin Garki Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, ko shakka babu, wannan ziyara ta Shugaba Hu Jintao zuwa wasu kasashen Afirka zai kara dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka, ba ma ga kasashen da ya ziyarta kawai ba.Wannan ziyara ta yi daidai da lokacin da ake bukatarta, saboda yanzu lokaci ne da kasashen da ya ziyarta ke fuskantar kalubale da agaji da kuma taimako. Hakika, wannan ziyara za ta tabbatar wa wadannan kasashen cewar kasar Sin tana tare da su a koda yaushe, kun san an ce, "abokin kuka ake gaya wa mutuwa". Da fatan wannan zumunci da ke tsakanin kasashenmu na Afirka da Sin za ta dada dorewa don samun nasara da kuma cin moriyar juna bisa harkokin yau da kullum na Duniya.

Akwai kuma malam Aminu Ahmad daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, sharhin da zan bayar a kan zuwan shugaban kasar Sin a Afirka, gaskiya wannan babban ci gaba ne, kuma ko a nan gida Nijeriya, ya kamata ku san cewa, mun fi sha'awar kasuwanci da 'yan kasar Sin, sabo da haka, wannan ziyara za ta kara mana dankon zumunci da kaunar juna, kuma Allah ya bar mu tare.

Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa. A shekara ta 1956, Sin ta kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Masar, abin da kuma ya nuna cewa, Sin da Afirka sun shiga wani sabon zamani wajen bunkasa huldar da ke tsakaninsu. Daga baya, kasashen Afirka da suka sami 'yancin kansu sun kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin daya bayan daya. A cikin shekaru 50 da suka wuce, Sin da Afirka suna mara wa juna baya a cikin harkokin duniya. A gun babban taron MDD da aka yi a shekarar 1971, an zartas da kuduri dangane da maido da kujerar sabuwar kasar Sin a MDD, kuma daga cikin kasashe 76 da suka kada kuri'ar amincewa, kasashe 26 sun zo ne daga Afirka. Bayan haka, sau 11 ne Sin ta murkushe shirye-shiryen batutuwan nuna adawa da kasar Sin da aka gabatar a gun taron hakkin bil Adama na MDD, sa'an nan sau 13 ne Sin ta murkushe yunkurin Taiwan na "komawa a MDD", bayan haka, Sin ta kuma cimma nasarar samun iznin karbar bakuncin wasannin Olympics na shekarar 2008 da kuma babban bikin baje koli na duniya na shekara ta 2010, kuma dukan wadannan ba za su iya rabuwa da tsayayyen goyon bayan da kasashen Afirka suka ba ta. A sa'i daya kuma, Sin tana kokarin sa kaimi ga gamayyar kasa da kasa da su dora muhimmanci a kan zaman lafiya na Afirka da bunkasuwarta, da kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su shiga harkokin duniya cikin daidaici. A kan maganar gyare-gyaren MDD kuma, Sin ta nuna goyon baya ga bai wa kasashe masu tasowa fifiko, musamman ma kasashen Afirka wajen kara wakilcinsu a MDD. A shekaru 50 da suka wuce, Sin da Afirka suna hadin gwiwa da juna a wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman al'umma da kuma neman ci gabansu. A cikin shekaru 50 da suka wuce, sahihin zumunci da zaman daidaici da moriyar juna da hadin kan juna da kuma samun ci gaba tare sun zama ka'idar da Sin da Afirka ke bi wajen yin mu'amala da hadin gwiwa da juna, haka kuma karfi ne da ke sa kaimi ga bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Afirka cikin dorewa. Muna imani da cewa, wannan rangadin da shugaban kasar Sin ya kai wa kasashen Afirka zai kara sada zumunci da kuma hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.(Lubabatu)