Ran 7 ga wata, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Afrika ta Kudu ya bayar da jawabi a Jami'ar Pretoria a karkashin lakabi haka "a inganta hadin kan kasar Sin da Afrika don sa kaimi ga raya zaman jituwa a duniya" domin duk samarin Afrika gaba daya. A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya bayyana ra'ayoyin kasar Sin a kan kara dankon aminci a tsakanin Sin da Afrika daga zuriya zuwa zuriya don sa kaimi ga raya duniya mai jituwa.
A yayin da shugaba Hu ke yin jawabi, da farko ya waiwayi hanyoyi da jama'ar kasar Sin da ta Afrika suka bi a cikin sama da shekaru 50 da suka wuce, don nuna wa juna goyon baya a cikin famarsu ta neman 'yan kan kasa da hadin kansu wajen farfado da su, da bai wa juna taimako sosai a cikin harkokin duniya. Ya ce, "ko da yake akwai nisa sosai a tsakanin Sin da Afrika, amma duk da haka tun fil azal ya kasance da aminci a tsakaninsu. A cikin dogon lokacin tarihi, jama'ar Sin da ta Afrika sun kulla aminci mai zurfi irin na kuddakud a tsakaninsu, Jama'ar kasar Sin suna takama da irin aminci da jama'ar Afrika ke nuna musu cikin sahihanci! Ko a da ko a yanzu ko kuma nan gaba, jama'ar Sin kyakkyawar aminiya ce mai zaman daidaici da amincewa ga jama'ar Afrika, kuma ita ce kawarsu a ke taimakon juna da moriyar juna da kuma samun nasara tare, sa'an nan kuma su 'yanuwa ne na kuddakud. Ya kamata, jama'ar Sin da ta Afrika su yi dankon amincinsu daga zuriya zuwa zuriya! Tabbas ne, za su ci gaba da samun aminci a tsakanindu daga zuriya zuwa zuriya!
Bayan haka shugaba Hu ya bayyana sakamakon da aka samu a gun taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin guiwar Sin da Afrika da aka yi a shekarar bara. Ya nanata cewa, gwamnatin kasar Sin ta bayyana manufofi da matakai guda 8 da za a ta dauka don kara ba da gudummuwa ga Afrika, da soke basussuka da kasashen Afrika masu fama da talauci sosai suka ci daga wajenta, da bude kofar kasuwanninta ga Afrika, da inganta hadin kanta da Afrika a fannin tattalin arziki da zaman al'umma da sauransu.
A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya kuma bayyana sakamakon da kasar Sin ta samu tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a shekarar 1978. Ya tisa magana cewa, "ana raya kasar Sin ne cikin zaman lafiya da jituwa da hadin kai kuma kofarta a bude take. Kasar Sin tana kokarin sosai wajen raya zaman jituwa a gida, kuma tana son yin kokari tare da kasashe daban daban wajen raya duniya mai zaman lafiya da wadatuwa da jituwa. Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen daga tutar zaman laraya da samun bunkasuwa da hadin kai, da aiwatar da manufar diplomasiya ta zaman lafiya da mulkin kai ba tare da tsangwama ba, za ta tsaya tsayin daka wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin zaman lafiya, da aiwatar da manyan tsare-tsare don samun nasara tare da moriyar juna."
Shugaba Hu ya jiku da cewa, samari makomar kasa da ta al'umma ne. Ya ce, kasar Afrika ta Kudu tana sa ran alheri gare ku samari, sa'an nan ana sanya ran alheri ga duk samarin Afrika yayin da ake farfado da ita. Samarin kasar Sin da na Afrika su ne babban karfi na dankon aminci a tsakanin Sin da Afrika, kuma su ne manyan masu raya duniya mai jituwa. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsaida kuduri a kan cewa, nan da shekaru uku masu zuwa, yawan daliban Afrika wadanda za su sami sikolashif daga wajenta zai karu daga 2,000 zuwa 4,000 a ko wace shekara.
Bayan da budurwa Tholoana Rose Neheke, dalibar sashen koyon aikin huldar kasa da kasa ta Jami'ar Pretoria ta saurari jawabin shugaba Hu, sai ta bayyana cewa, "na yi matukar farin ciki da samun damar saurarar jawabin shugaba Hu, jawabinsa wani jawabi ne mai muhimmanci sosai. Yanzu kasar Sin kasa ce matashiya mafi girma a duniya, kasar Afrika ta Kudu kuwa kasa ce da ke shugabancin nahiya mai yawan kasashe masu tasowa a duniya, bisa matsayinsu ne, hulda da ke tsakaninsu tana da muhimmanci sosai, za su taka muhimmiyar rawa cikin harkokin duniya ta hanyar hadin kansu. Tana fatan kasashen Sin da Afrika ta Kudu za su sami makomansu mafi kyau. (Halilu)
|