Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 18:41:48    
Tattaunawa tsakanin shugaban kasar Sin da masu masana'antun kasar Sin da ke a Afrika

cri

Kafin shugaba Hu Jintao ya sauka kasar Afrika ta Kudu, ya halarci taron tattaunawa tare da wakilan masana'antun kasar Sin a kasashen Afrika da aka shirya a kasar Namibiya a ran 6 ga wata, inda ya bayar da jawabi mai muhimmanci. A cikin jawabinsa, shugaba Hu ya nuna cewa, makasudin ziyarar da yake yi yanzu a Afrika, shi ne domin nuna wa aminanmu na Afrika da gamayyar kasa da kasa cewa, ko shakka babu, kasar Sin za ta cika alkawarinta na yin hadin guiwa da kasashen Afrika, kuma cikin daidaici da sahihanci, Sin da Afrika suna hadin guiwarsu ne bisa halin da ake ciki, kuma suna samun sakamako mai kyau.

Kasar Sin babbar abokiyar Afrika ce a fannin cinikayya. Bisa sabuwar kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan kudi da aka samu daga wajen cinikayya a tsakanin Sin da Afrika ya kai dalar Amurka biliyan 55 a shekarar 2006, wato ke nan ya karu da kashi 40 cikin dari bisa na shekarar 2005. Ya zuwa karshen shekarar bara, jimlar kudin jari da kasar Sin ta zuba a Afrika ya kai dalar Amurka miliyan 6640, ayyuka da take zuba musu jari suna kasashen Afrika 49. A ran 6 ga wata da safe, wato jajiberen ranar da zai gama ziyarar aikinsa a kasar Namibiya, shugaba Hu ya halarci taron tattaunawa tare da wakilan kamfanonin kasar Sin da masana'antunta da ke a Afrika. A gun taron, bayan da shugaba Hu ya saurari ra'ayoyi da shawarwari da wakilan wadannan kamfanoni da msana'antu suka gabatar , ya nuna yabo cewa, wadannan masu aikin masana'antu wadanda ke nuna kwazo da himma wajen yin harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afrika tsoffin 'yan Afrika ne. Ya ce, "a farkon sabuwar shekarar nan, na zabi Afrika don yin ziyara a karo na farko, makasudinta shi ne domin inganta amincin gargajiya a tsakanin Sin da Afrika, da tabbatar da sakamako da aka samu a gun zaman Beijing na taron dandaklin tattaunawa a kan hadin guiwar Sin da Afrika, da kara hadin guiwar bisa halin da ake ciki, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da nuna wa aminanmu na Afrika da gamayyar kasa da kasa cewa, ko shakka babu, kasar Sin za ta cika alkawarinta na yin hadin guiwa da kasashen Afrika, kuma cikin daidaici da sahihanci, Sin tana hadin kanta da Afrika ne bisa halin da ake ciki, suna samun sakamako mai kyau."

Shugaba Hu ya kara da cewa, Afrika nahiya ce mai yawan kasashe masu tasowa, don haka yalwata dangantakar aminci da hadin kai a tsakaninta da kasashen Afrika tana da muhimmanci sosai ga kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. Ya ce, "bunkasuwar zaman jituwar duniya yana da nasaba da bunkasuwar zaman jituwa a hulda da ke tsakanin Sin da Afrika. Tabbas ne, bunkasa hulda a tsakanin Sin da Afrika cikin jituwa zai samar da kyawawan sharuda ga tabbatar da zaman jituwar duniya, hadin kansu a fannin tattalin arziki babban karfi ne da ke bunkasa dangantakar abokatanka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare, kuma ginshiki ne don zurfafa ayyukan Afrika, abin da ake bukata wajen kara bunkasa irin wannan dangantakar, shi ne Sin da kasashen Afrika su sami ra'ayi bai daya, su inganta hadin kansu, kuma masana'antunsu su yi kokari tare."

Yanzu, kasashen Afrika dukanninsu suna mayar da bunkasuwar tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a bisa matsayin babban aikinsu. Yayin da ake inganta hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arziki, masana'antun kasar Sin da ke a Afrika suna sauke da babban nauyi da ke bisa wuyansu, don haka shugaba Hu ya bayyana cewa, "na daya, su nace ga tunawa da nauyi da ke bisa wuyansu sosai, su bauta wa babbar manufa, na biyu, su nace ga mayar da kwarjini da inganci a gaban kome, na uku ya kamata, su nace ga ba da taimakonsu wajen tabbatar da zaman jituwa da kawo zaman alheri ga jama'a."

Wakilan masana'antun kasar Sin a Afrika sun bayyana daya bayan daya cewa, za su yi kokari wajen kara ba da taimakonsu don inganta hadin kai a tsakanin Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya. (Halilu)