Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 18:32:50    
Shugaban Sudan ya nuna godiya kan goyon bayan da Sin ta ba ta

cri
A ran 6 ga wata, shugaban kasar Sudan, Omar Hassan Ahmed al-Bashir ya bayyana a birnin Khartoum cewa, Sudan ta nuna babban yabo a kan matsayin da kasar Sin ke dauka na inganta hadin gwiwar da ke tsakaninta da Sudan a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da dai sauransu, kuma ta nuna godiya kan goyon bayan da kasar Sin ke ba ta a dandalin duniya.

A gun babban taron hadin kan kungiyoyin kwadago na kasashe daban daban da jama'ar Sudan da aka bude a ran nan, Mr.Al-Bashir ya ce, Sin tana kokarin bayar da taimakon jin kai ga jama'ar da ke shiyyar Darfur, kuma tana yin kira ga bangarori daban daban da rikicin ya shafa da su bi hanyar shawarwari da kuma zaman lafiya, don sa kaimi ga daidaita batun Darfur tun da wuri, kuma ya nuna babban yabo da sahihiyar godiya ga kasar Sin da kuma ziyarar da shugaban kasar, Mr.Hu Jintao ya kai wa Sudan ba da dadewa ba.(Lubabatu)