Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 17:19:23    
Shugaba Hu Jintao ya yi shawarwari da takwaransa na Afirka ta Kudu

cri

Ran 6 ga wata, a birnin Pretoria, hedkwatar kasar Afirka ta Kudu, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Thabo Mvuyelwa Mbeki. Bangarorin 2 sun bayyana cewa, za su ci gaba da daidaitawa da raya dangantakar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, da kuma daukaka ci gaban huldar aminci da ke tsakaninsu daga manyan tsare-tsare bisa tushen yin zaman daidai wa daida da moriya juna da samun bunkasuwa tare.

A gun shawarwarin da aka yi, shugaba Hu ya shawarci shugabannin kasashen Sin da Afirka ta Kudu da su rika tuntubar juna a tsakanin bangarori 2 da kuma bangarori daban daban. Ya kara da cewa, kasar Sin na maraba da masana'antun kasar Afirka ta Kudu da su kafa masana'antu a kasar Sin. Gwamnatin Sin kuma tana sa kaimi da kuma goyon bayan masana'antun Sin da su zuba jari a kasar Afirka ta Kudu, da kuma yin hadin gwiwa kan manyan ayyuka. Ban da wannan kuma, shugaba Hu ya ba da shawara ga bangarorin 2 da su nemi hada kansu domin moriyar juna a fannonin aikin horar da sana'a da yaki da laifuka da dai sauransu, za su kara hadin gwiwarsu a cikin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin duniya, za su sa kaimi kan bunkasa ra'ayin kasancewar rukunoni da yawa da huldar da ke tsakanin kasashen duniya ta fuskar dimokuradiyya da kuma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa bai daya.

A nasa bangaren kuma, Mr. Mbeki ya amince da shawarar da shugaba Hu ya gabatar wajen daukaka ci gaban huldar abokantaka da ke tsakanin kasarsa da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na daya daga cikin muhimman aminai ga kasar Afirka ta Kudu a fannin tattalin arziki. Yin tattaunawa da hadin gwiwa da kasar Sin dukiya ce ga kasar Afirka ta Kudu wajen daidaita kalubale a fannin siyasa. Yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka na da muhimmanci sosai wajen farfado da kasashen Afirka.(Tasallah)