Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 16:54:18    
Wasannin motsa jiki kan kankara na samun saurin ci gaba a Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin

cri
Yankunan Hong Kong da Macao da kuma Taiwan na kasar Sin na cikin wurare masu zafi, sun dade suna fuskantar takurawa ta fuskar yanayi, a sakamakon haka, sun gamu da matsaloli da yawa wajen yada wasannin Olympic na lokacin hunturu. Amma a lokacin da yake harhada labarai a gun taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Asiya a karo na 6 a Changchun na kasar Sin, wakilinmu ya gano cewa, saboda a cikin shekaru misalin 10 da suka wuce, an komo da Hong Kong da Macao a hannun kasar Sin, kuma an yi ta yin mu'amala a tsakanin jama'ar gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, shi ya sa wasannin motsa jiki kan kankara ya sami babban ci gaba a wadannan yankuna 3, yana kuma kara samun goyon baya daga jama'ar yankunan 3.

Malam Huang Yongxi mai shekaru 49 da haihuwa dan wasa ne mafi tsufa a cikin dukan 'yan wasan Hong Kong na kasar Sin da suka halarci taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Asiya na karo na 6. A matsayinsa na mai tsaron gida a cikin gasar wasan kwallon gora kan kankara , malam Huang ya ga tarihin wasan kwallon gora kan kankara a Hong Kong a idonsa. Ya bayyana cewa,'An fara yin hadaddiyar gasar wasan kwallon gora kan kankara a Hong Kong a shekara ta 1996, a lokacin nan kungiyoyi 4 ne kawai suka shiga wannan hadaddiyar gasa, yawan 'yan wasan kwallon gora kan kankara ya kai kimanin 100, a cikinsu kuma akwai wadanda suka zo daga kasashen waje, suna sha'awar wannan wasa sosai, shi ya sa sun tafiyar da wani kamfani, su nemi masu ba da kudade don shirya wannan hadaddiyar gasa. Yanzu an raba kungiyoyin wasan kwallon gora kan kankara zuwa rukunoni 4 a Hong Kong, wato na A zuwa na D. Kungiyoyi masu shiga gasanni na rukunin A sun fi nuna kwarewa. Mutanen kasashen waje da yawa su ma sun shiga gasannin wannan rukuni, wasu daga cikinsu kuma sun taba shiga hadaddun gasanni na kasashen waje. Wasu jami'o'i sun kuma aike da kungiyoyinsu, wadanda suka yi fintikau.'

Wasan kwallon gora kan kankara na cikin wasannin motsa jiki na lokacin hunturu tsakanin kungiya kungiya da ba safai a kan gansu ba, amma yana bukatar kudi da yawa, in an kwatanta shi da wasannin kwallon kafa da na kwando. A kan kashe kudin da yawansa ya wuce kudin Hong Kong dala dubu 10 wajen sayen kayayyakin wasanni, sa'an nan kuma kudaden da ake amfani da su wajen aikin horaswa da yin hayar filin wasan suna da yawa, dukan wadannan sun matsa wa wani iyali babbar lamba. Amma iyayen yaran da suke kishin wasannin motsa jiki kan kankara sun fi bayar da lokaci da kuzari, a maimakon kudi. Madam Du, mamar 'yar wasan gudun kankara na salo-salo Guo Jiahui na Macao na kasar Sin ta gaya mana cewa,'Mu iyaye muna rakiyar 'ya 'yanmu zuwa wajen samun horo, mun ba da gudummowarmu sosai ta fuskar lokaci da kuzari. 'Ya 'yanmu su kan tashi da karfe 4 na safe, a kan horar da su daga karfe 5 zuwa karfe 6 ko 7, daga baya sun je karatu, su kan ci gaba da horo da karfe 7 ko karfe 8 na dare, bayan haka kuma sun koma gida su kammala aikin gida. A ganina, sun sha wahala sosai.'

Ko da yake yana kasancewa da matsaloli har zuwa yanzu, amma wadannan wasannin kan kankara suna kara samun amincewa da karbuwa daga matasa saboda wadannan masu kishinsu, wadanda suka jure wahaloli suka ci gaba da yinsu.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, saboda Hong Kong da Macao sun komo cikin kasar Sin mahaifiya, haka kuma lardin Taiwan da babban yankin Sin sun kyautata cudanya a tsakanin jama'arsu, shi ya sa sun sami goyon daya da tallafawa da yawa daga babban yankin Sin a fannin raya wasannin kan kankara. Madam Li Liping, mai horas da wasan gudun kankara na salo-salo ta fara horar da 'yan wasa a Macao bayan da ta ritaya. A lokacin da take zantawa da wakilinmu, ta waiwayi abubuwan da suka faru a shekarun nan da suka wuce a lokacin da take Macao, ta ga ci gaban yada wannan wasanni, tana kuma ganin cewa, ya kasance da fata na kara raya wannan wasanni.

Bullowar 'yan wasa wadanda shekarunsu ba su da yawa ta jawo hankulan mutane, ta kuma kara wa yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan aniyar raya wasannin kan kankara. Mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympic na Asiya kuma shugaban kwamitin wasannin Olympic na Hong Kong na kasar Sin Huo Zhenting ya yi wa wakilinmu bayani kan makoma, ya ce,'Ina ganin cewa, babban yankinmu zai ci gaba da ba mu taimako, wasannin kan kankara za su sami bunkasuwa a Hong Kong.'(Tasallah)