Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 16:54:18    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (01/02-07/02)

cri
Ran 1 ga wata, a nan Beijing, wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, tun daga ran 28 ga watan Agusta na shekarar bara da aka fara daukar masu aikin sa kai domin gasannin taron wasannin Olympic na Beijing da na nakasassu a hukunce, har zuwa karshen watan Janairu na shekarar nan da muke ciki, mutane fiye da 320,000 da suka zo daga babban yankin kasar Sin sun yi rajista. Za a tabbatar da masu aikin sa kai na rukuni na farko kafin watan Agusta na shekarar bana.

Akwai wani labari daban daga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, an ce, a ran 1 ga wata, mataimakin shugaban sashen aikin injiniya da muhalli na wannan kwamiti Yu Xiaoxuan ya bayyana cewa, tabbas ne Beijing za ta cika alkawarin da ta yi a fannin ingancin yanayi a lokacin da take neman samun damar shirya taron wasannin Olympic. Ya kara da cewa, Beijing tana kyautata ingancin iska sannu a hankali saboda tana daukar matakai a jere don sarrafa aikace-aikacen gurbata iska. Ban da wannan kuma, shugaban sashen rarraba kayayyaki a zahiri Yan Ligang ya bayyana cewa, an riga an aiwatar da matakai don samun iznin shigo da kayayyakin taron wasannin Olympic na Beijing daga kwastan, yanzu kayayyaki na rukuni na farko sun iso Beijing.

Ran 4 ga wata da dare, an rufe taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Asiya na karo na 6 a birnin Changchun da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Kasar Sin ta zama ta farko a fannonin samun lambobin yabo da kuma lambobin zinariya a tsakanin dukan kasashe da yankunan da suka shiga wannan taron wasannin motsa jiki. Za a yi taron wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Asiya mai zuwa a birnin Almaty na kasar Kazakhstan.

Ran 2 ga wata, Hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta ba da wata sanarwa a birnin Zurich, inda ta ce, kungiyoyi 14 sun sami damar shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata a karo na 5 da za a yi a watan Satumba na shekarar nan a nan kasar Sin, akwai sauran kungiyoyi 2, wadanda suka nemi samun irin dama. Kungiyoyin kasashen Jamus da Sin sun zama gogaggun kungiyoyi ne a cikin rukuni na A da na D.(Tasallah)