Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 10:47:32    
Kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun bayar da sanarwar hadin kai

cri

A ran 6 ga wata, kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun bayar da sanarwar hadin kai a birnin Pretoria, babban birnin siyasa na kasar Afirka ta Kudu, inda bangarorin biyu suka amince da duba da raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, da kuma yin kokari tare wajen inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Kudu zuwa wani sabon mataki.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince da kiyaye yin mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da kuma yin musanyar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakaninsu da kuma al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu, ta yadda za a iya sa kaimi ga samun amincewar juna da kuma moriyar juna. Ban da wannan kuma bangarorin biyu za su sa kami ga kwamitocin kula da dangantaka a tsakanin bangarori biyu na kasashensu wajen bayar da amfaninsu, ta yadda za su iya zama wani muhimmin tsari wajen inganta dangantakar da ke tsakanin bangarori biyu. Bugu da kari kuma bangarorin biyu za su dukufa kan karfafa zuciyar yin cinikayya tsakaninsu bisa tushen tabbatar da kafa dangantakar cinikayya cikin daidaici don moriyar juna tsakaninsu. Kazalika kuma kasashen biyu za su kara kwarin gwiwar kamfanoninsu wajen neman samun damar raya cinikayya a kasashen biyu.

Ban da wannan kuma sanarwar ta bayyana cewa, bangarorin biyu sun tsai da kudurin ci gaba da yin cudanya da hadin kai a cikin MDD da kungiyar WTO da sauran kungiyoyin duniya, da kuma daidaita matsayinsu wajen samun bunkasuwa da kawar da talauci da kuma rikicin da ke tsakanin shiyya-shiyya, ta yadda za su iya kiyaye hakkin kasashe masu tasowa.(Kande Gao)