Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 02:55:33    
Kasar Sin za ta kara yin hadin guiwa da kasashen Afirka

cri

A ran 6 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta yi kokarin kara yin hadin guiwa da kasashen Afirka a fannoni daban-daban, kuma za ta daga matsayin irin wannan hadin guiwa.

Mr. Hu ya fadi haka ne a birnin Windhoek, fadar kasar Namibiya lokacin da yake halartar taron tattaunawa da wakilan masana'antu masu jarin kasar Sin da ke kasashen Afirka. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara habaka mahadar yadda kasar Sin da kasashen Afirka za su iya samun moriya tare, kuma za ta kara karfin yin hadin guiwar moriyar juna tsakaninsu. A waje daya kuma za ta taimaki kasashen Afirka wajen kyautata karfinsu na dogara da kansu wajen neman bunkasuwa. Sakamakon haka, jama'ar Afirka za su iya samun moriya a zahiri daga irin wannan hadin guiwa.

Hu Jintao ya ce, yanzu kasashen Afirka sun sanya aikin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a a gaban duk ayyukan da suke yi. Yin hadin guiwar tattalin arziki muhimmin karfi ne da ke raya dangantakar abokanta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka bisa manyan tsare-tsare.

Hu Jintao yana fatan masana'antu masu jarin kasar Sin wadanda suke kasashen Afirka za su iya ci gaba da bin ka'idojin kare suna da ingancin kayayyakinsu, kuma za su iya zama tare da zaman al'ummar wurin cikin jituwa domin kara raya hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Sanusi Chen)