Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 21:14:15    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi ziyara a kasar Namibiya

cri

Yanzu ga wani rahoton musamman game da Rangadin sada zumunta da hadin guiwa da shugaban kasar Sin Hu Jintao ke yi a kasashen Afirka 8. Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Namibiya Hifikepunye Pohamba ya yi masa ne, a ran 5 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Windhoek, fadar kasar Namibiya domin fara yin ziyararsa ta aiki a kasar. Yanzu ga wani rahoton da wakiliyarmu ta aiko mana daga birnin Windhoek.

Lokacin da jirgin sama na musamman da Hu Jintao yake dauka ya sauka a filiin jirgin sama na Windhoek, jama'ar Namibiya sun shirya bikin waka da raye-raye domin maraba da zuwan wannan muhimmin bakon da ya zo daga kasar Sin wadda take nisa da kasar Namibiya fiye da kilomita dubu 10.

A gun liyafar maraice da shugaba Pohamba ya shirya masa, Mr. Hu Jintao ya bayar da wani jawabi, inda ya yaba wa kakkarfan zumuncin da ke kasancewa a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Mr. Hu ya ce, "Lokacin da kasar Namibiya take yin gwagwarmaya domin neman ikon mulkin kai, kasar Sin tana nuna mata goyon baya kwarai. Bayan da kasar Namibiya ta samu 'yancin kai, kasar Sin abokiyarta ce ta hadin guiwa. A cikin shekaru 17 da suka wuce, tun bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, hadin guiwar da ke tsakanin kasashensu ta samu ci gaba a fannonin tattalin arziki da cinikayya da ilmi da kiwon lafiya da al'adu da dai makamatansu. Jama'ar kasashen biyu ma suna kara samun fahimtar juna da sada zumunta a tsakaninsu. Game da al'amuran kasa da kasa, bangarorin biyu suna amincewa da juna da nuna wa juna goyon baya a kullum. Kasar Namibiya tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak, kuma tana nuna goyon bayan yunkurin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya. Ba za mu manta ba, lokacin da kasar Sin take bukatar goyon baya daga kasar Namibiya, gwamnati da jama'a na kasar Namibiya suna nuna wa kasar Sin goyon baya ba tare da wata-wata ba. A ganin kasar Sin, kasar Namibiya aminiya ce da za ta iya amincewa da ita a kullum."

A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, an ci nasarar shirya taron koli na dandalin tattaunawar hadin guiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, an kuma sami sakamako masu dimbin yawa. Hu Jintao ya ce, muhimmin burin ziyararsa da yake yi a kasar Namibiya shi ne, zai yi shawarwari da shugabannin kasar kan yadda za a tabbatar da sakamakon da aka samu a gun wannan taron koli. A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya sanar da jerin matakai domin nuna wa kasar Namibiya goyon baya wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'arta. Mr. Hu ya ce, "Gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin cewa, za ta samar wa kasar Namibiya wasu kudaden kyauta da wasu rancen kudin da za a nemi kudin ruwa kadan. A waje daya kuma, a cikin shekaru 3 masu zuwa, wato tsakanin shekarar 2007 da ta 2009, kasar Sin za ta samar wa kasar Namibiya wasu rancen kudade masu gatanci da za su kai kudin Renminbi yuan biliyan 1 da wasu rancen kudade masu gatanci da za su kai dalar Amurka miliyan dari 1 domin fitar da kayayyakin kasar Namibiya."

Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi kan manyan masana'antun kasar Sin da su zuba jari a kasar Namibiya da kara yin hadin guiwa a fannonin cinikayya da raya ayyukan yau da kullum da aikin gona. Haka kuma, za ta dauki matakai domin kara shigar da kayayyaki daga kasar Namibiya da dai sauransu.

A cikin nasa jawabin, shugaba Pohamba na kasar Namibiya ya bayyana cewa, jama'ar Namibiya ba za ta manta ba, lokacin da suke gwagwarmayar neman 'yancin kai da raya tattalin arziki da zaman al'umma, gwamnati da jama'a na kasar Sin suna tsayawa tare da su, kuma suna nuna goyon bayansu sosai. Kasar Namibiya tana darajanta amincin da ke tsakanin kasashen biyu, kuma tana kokarin habaka da karfafa hadin guiwar moriyar juna a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu. Ya jaddada cewa, "Gwamnatin Namibiya tana tsayawa kan manufar Sin daya tak gadan gadan. Taiwan wani yanki ne da ba za a iya kebe shi daga kasar Sin ba. Gwamnatin kasar Nambiya tana kuma goyon bayan yunkurin tabbatar da ikon mulkin kai da cikakken yankunanta da kasar Sin take yi. Tana kuma nuna wa kasar Sin goyon baya domin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya." (Sanusi Chen)