A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku da bayani kan cewa, samun kiba fiye da kima ga matan da suka daina haila zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar mama, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, ana tafiyar da ayyukan lura da yara mata a jihar Guizhou don hana rashin daidaito tsakanin jinsin maza da mata.
wani sabon nazarin da masu ilmin kimiyya da fasaha na kasar Amurka suba yi ya bayyana cewa, idan mata sun samun kiba fiye da kima bayan da suka daina haila, to sun fi saukin kamu da ciwon sankarar mama. Kuma idan nauyin jikinsu ya kara karuwa, to za a kara hadarin mutuwa sakamakon ciwon sankarar mama.
Kafin wannan, wani nazari ya taba bayyana cewa, ciwon da ka kamu da shi sakamakon samun kiba fiye da kima yana da nasaba da ciwon sankarar mama. Wannan nazarin da Maria Gammon na jami'ar North Carolina ta kasar Amurka ta yi ya tabbatar da irin wannan dangantakar da ke tsakanin cuttuttukan biyu. A 'yan kwanakin nan da suka gabata, ta ba da rahoto a gun taron shekara-shekara na kungiyar nazarin cuttuttuka da aka kamu da su sakamakon samun kiba fiye da kima ta Amurka da aka yi a birnin Boston, cewa a cikin matan da suka daina haila, yiyuwar kamu da ciwon sankarar mama ga wadanda suka samu kiba fiye da kima ya karu da kashi 75 cikin dari idan an kwatanta ita da wadanda suke da jiki sosai.
Ban da wannan kuma Madam Gammon ta bayyana cewa, dole ne mata su gane cewa, idan ki kamu da ciwon sankarar mama, kuma nauyin jikinki ya ci gaba da karuwa bayan da shekarunki ya kai 50 da haihuwa, to za ki fi saukin mutuwa.
Yanzu za mu ba ku wani labari daban game da ciwon sankarar moma. Wani sabon nazarin da masu ilmin kimiyya da fasaha na kasashen Turai suka yi ya bayyana cewa, game da mata masu kamu da ciwon sankarar mama wadanda aka yi musu tiyata don kare mamansu, yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi zai ba da taimako wajen shawo kan sake aukuwar ciwon.
Masu ilmin kimiyya da fasaha sun raba mata 7300 da aka yi musu tiyata don kare mamansu cikin kungiyoyi biyu ba tare da aka yi zabi ba, kuma an yi jiyya ga matan da ke cikin wata kungiya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi, amma ba a yi haka ba ga matan da ke cikin kungiya dayan. Sakamakon nazarin ya bayyana cewa, idan ba mata wadanda kwayar sankara ta ratsa karinsu ba su karbi dabarar yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi ba, to kashi 46.5 bisa dari daga cikinsu ciwon sankarar mama da suka kamu da shi zai sake aukuwa. Amma jimlar ta kai kashi 13 bisa dari kawai ga wadanda suka karbar yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi.
Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, ana tafiyar da ayyukan lura da yara mata a jihar Guizhou don hana rashin daidaito tsakanin jinsin maza da mata.(Kande)
|