Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 16:00:43    
Cibiyar harbar taurarin dan Adam ta Xichang

cri

Birnin Xichang yana kwarin dutse mai suna Liangshan da ke da nisan kilomita 65 daga kudu maso yammacin lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin. A nan ne aka gani cibiyar harbar taurarin dan Adam ta kasar Sin, saboda haka ana ma kiran birnin nan da wani suna daban wato 'birnin zirga-zirgar sararin samaniya'.

Cibiyar harbar taurarin dan Adam ta birnin Xichang ta kasar Sin ita ce sansani mafi girma na harbar taurarin dan Adam irin na sabon salo a duk nahiyar Asiya. Tana amfani da kayayyakin aikinta na zamai wajen harba manyan taurarin dan Adam da kumbuna. Sa'an nan kuma, cibiyar nan fili ne mafi girma na harba taurarin dan Adam wanda aka bude kofarta ga kasashen waje, ta sha harba taurarin dan Adam domin kasashen waje. Taurarin dan Adam da aka harba daga cibiyar nan sun hada da taurarin dan Adam na watsa labaru ta rediyo da telebijin da na sadarwa da binciken yanayin sararin samaniya da dai sauransu. Tun bayan da aka harba tauraron dan Adam daga cibiyar harbar taurarin dan Adam ta birnin Xichang a karo na farko a shekara ta 1984, an yi amfani da rokoki masu samfurin Changzheng-3 da E2 da kuma A3 wajen harba taurarin dan Adam da yawansu ya wuce 10 tare da nasara.

Tun daga watan Disamba na shekara ta 2003, ba ma kawai masu yawon shakatawa na yau da kullum suna iya shiga filin harba taurarin dan Adam ta birnin Xichang don ganmma idonsu yadda aka harba tauraron dan Adam ba, har ma za su iya jin karar da tauraron dan Adam ke yi yayin da yake shawagi a sararin samaniya. Amma yawan masu yawon shakatawa da za su sami damar kallon harba tauraron dan Adam da za a yi a lokaci guda ba za su wuce 5000 ba, saboda wurin de ke kewayen filin matsattse ne.(Tasallah)