Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 20:44:45    
Manyan jaridun kasar Sudan sun yaba wa ziyarar da Hu Jintao ya kai wa kasar

cri

A ran 5 ga wata, bi da bi ne manyan jaridun kasar Sudan suka bayar da sharhinsu, inda suka yaba wa nasarorin da aka samu a gun ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai wa kasar Sudan daga ranar 2 zuwa ranar 3 ga wata.

Muhimmiyar Jaridar 'Al-Raay Al-Am' ta Sudan ta bayyana cewa, a lokacin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ke ziyarar aiki a kasar Sudan, bangarorin biyu sun daddale yarjejeniyoyi a jere domin hada kansu, ta haka sun kara raya dangantakarsu ta abokantaka da hadin kai. Wannan jarida ta ci gaba da cewa, kasar Sin tana nuna goyon baya ga sha'anin shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a Sudan, kuma ta bayar da taimako sosai a kan yunkurin shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur ta Sudan.

Wata babbar jarida daban 'Al-Ayaam' ta bayyana cewa, ziyarar Hu ta zama wata muhimmiyar ishara ga dangantakar aminci da hadin kai a tsakanin kasashen Sudan da Sin, kuma za ta bayar da taimako sosai a kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sudan da kuma tabbatar da zaman karko a kasar.(Danladi)