Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 15:45:01    
Takaitaccen bayani game da kabilar Maonan

cri

Kabilar Maonan tana daya daga cikin kananan kabilun da suke da jama'a kadan. Amma ko da yake kabilar Maonan ba ta da mutane da yawa, ta yi suna sosai domin dogon tarihi da al'adun musamman. Yawancin mutanen kabilar Maonan suna zama a gandumar Huanjiang da ke jihar Guangxi a kudancin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Maonan ya kai dubu 107. Suna amfani da yaren Maonan, amma babu kalma. Domin sun dade suna zama tare da kabilun Han da zhuang, sun iya harshen Zhuang da Han, wato harshen Sinanci.

Mutanen kabilar Maonan suna kiran kansu "A Nan", ma'anar shi ita ce "Mutane ne da ke zama a wannan wuri".

A da, mutanen kabilar Maonan suna zama a yankunan da ke cikin tsaunuka, ba su da isassun gonaki. Amma suna da himma da kwazo da hankali da darajantar da gonaki wajen aikin gona. Mutanen kabilar Maonan su kan fadi cewa, "Gonaki suna fitar da zinariya, gona kadan ma za mu yi noma." A kudancin yankin kabilar Maonan, an sare gonaki a kan tsaunuka. Mutanen kabilar Maonan sun dade suna aikin gona, sun kuma yi amfani da kayan aiki na karfe tun da wuri. Bugu da kari kuma suna kiwon shanu, kuma suna sayar da shanu har a birnin Shanghai da Hong Kong.

Mutanen kabilar Maonan suna da himma da kwazo da hankali. A cikin dogon lokacin da ya wuce, sun kirkiro al'adu iri iri. Suna da tatsuniyoyi da almara da yawa.

A waje daya kuma, mutanen kabilar Maonan sun kware kan kera kayayyaki da bamboo, kamar su hula ta bamboo da mutum-mutumin bamboo da dabobbi iri iri na bamboo.

Mutane wadanda suke da kakanin-kakani daya, suna zama tare. Suna gina kauyensu ne a karkarshin wani tsauni. Yawancin irin wannan kauye yana da gidaje kimanin 10. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Maonan, maza ko mata sun fi son sanya tufafi masu launin shudi da baki.

Bisa al'adar kabilar Maonan, kowane saurayi yana iya auren mace daya. A da, iyaye ne suke shirya yaransu aure. Bayan da aka yi bikin aure, ba dole ba ne amariya ta yi zama a gidan ango.

Mutanen kabilar Maonan suna bin addinin Daoist, wani addinin gargajiya na kasar Sin. Suna kuma girmama dodanni iri iri. (Sanusi Chen)