Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-04 21:11:44    
Mr Hu Jintao, shugaban Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na Zambiya Levy Mwanawasa

cri

A ran 3 ga wata, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Zambiya Mr Levy Mwanawasa a birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambiya. Inda suka sami ra'ayi daya a kan kara nuna fahimta da amincewa a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Zambiya, da kara inganta amincin gargajiya da hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu.

Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasashen biyu har cikin shekaru 42 da suka wuce, an bunkasa huldar kamar yadda ya kamata. Gwamnatin kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasar Zambiya bisa kokarin da take yi wajen yaki da talauci da bunkasa harkokin tattalin arziki, tana son yin duk abubuwa da take iya yi wajen bai wa kasar Zambiya taimako. Ya kuma tsai da kuduri a kan kafa yankin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin a kasar Zambiya.

Daga wajensa, Mr Mwanawasa ya ce, ana bunkasa kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen Zambiya da Sin bisa tushen amincewa da juna da aminci da hadin kai. Kasar Sin tana aiwatar da alkawarin da ta dauka a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika a tsanake. Kasar Zambiya za ta yi kokari wajen yalwata huldar aminci da hadin kai a tsakaninta da kasar Sin.

A gun liyafar da aka shirya don girmama shi a wannan rana, Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, ana hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afrika cikin daidaici da moriyar juna. Ya ce, kasar Sin za ta yi kokari wajen shigowa da kayayyaki masu yawa daga Afrika, ta dauki matakai wajen rage harajin kwastan mai yawa da take bugawa a kan wasu kayayyaki da take shigowa daga Afrika, don daidaita matsalolin cinikayya da abin ya shafa kuma suke jawo hankulan wasu kasashen Afrika. (Halilu)