Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-04 21:07:34    
Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar dokoki ta kasar Zambiya da tsohon shugaban kasar

cri

A ran 4 ga wata a birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambiya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar dokoki ta kasar Zambiya Amusaa K. Mwanamwambwa da tsohon shugaban kasar Kenneth David Kaunda. A ran nan kuma, kasashen biyu sun bayar da wata sanarwa ciki hadin gwiwarsu, inda suka bayyana cewa, za su kara hadin kansu a fannoni daban daban.

A yayin da yake ganawa da Mr Mwanamwambwa, shugaba Hu ya ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar dokoki ta kasar Zambiya suna da kyakkyawar dangantakar hadin kai a tsakaninsu, kasar Sin tana son kara yin mu'amala da hukumomin kafa dokoki na kasar Zambiya.

A ran nan kuma, bangarorin biyu sun bayar da wata sanarwar tare, inda suka bayyana cewa, bangarorin biyu gaba daya sun yarda da kara yin shawarwari a tsakaninsu da kara hadin kansu, za su kara yin kokari domin ciyar da dangantakar abokantaka a tsakaninsu gaba.(Danladi)