Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-04 18:29:09    
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Zambia

cri

Jiya a birnin Lusaka, babban birnin kasar Zambia, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Zambia, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar, Mr.Levy Patrick Mwanawasa, inda bangarorin biyu suka cimma daidaito kan kara fahimtar juna da amincewa da juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu da bude kyakkyawar makomar huldar da ke tsakaninsu.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun gana da manema labaru. Mr.Hu Jintao ya ce, a cikin shekaru 42 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Zambia, huldar da ke tsakanin kasashen biyu bunkasa ta yi lami lafiya. Ya ce,"Ya kasance da zumuncin gargajiya a tsakanin jama'ar Sin da ta Zambia. A cikin 'yan shekarun baya, bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi tare, an kuma kara karfafa dankon zumuncin. Yawan cinikin da ke tsakanin bangarorin biyu ya bunkasa da sauri. A shekarar da ta gabata, yawan kudin cinikin da ke tsakanin kasashen biyu ya riga ya zarce dallar Amurka miliyan 370. Sin ta zo ta uku a wajen zuba jari a kasar Zambia, tana zuba jari a fannonin noma da sadarwa da raya manyan ayyuka da hakar ma'adinai da harkar kudi da dai sauransu. Bayan haka, bangarorin biyu suna kuma tuntubar juna da kuma hadin gwiwa da juna a cikin harkokin duniya, suna kokarin kiyaye hakkin kasashe masu tasowa da moriyarsu kamar yadda ya kamata. Gwamnatin Zambia tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana tallafawa harkar neman dinkuwar kasar Sin, tana kuma ba mu goyon baya a harkokin duniya, Sin tana farin ciki da samun Zambia a matsayin wata abokiyar arziki da kuma 'yar uwarta."

Mr.Hu Jintao ya ci gaba da cewa, a gun taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka da aka yi a watan Nuwamba da ya gabata a birnin Beijing, gwamnatin kasar Sin ta sanar da manufofi takwas dangane da inganta hakikanin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da kuma nuna goyon baya ga bunkasuwar kasashen Afirka. Sin tana dora muhimmanci sosai a kan tabbatar da wadannan nasarorin da aka samu a gun taron, kuma za ta dauki matakai tare da kasashen Afirka da abin ya shafa, don tabbatar da wadannan manufofi da matakai tun da wuri, ta yadda za a kawo wa jama'ar Afirka alheri. Ya ce ,"Domin tabbatar da nasarorin da aka samu a gun taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka, Sin ta tsai da kudurin soke rancen kudi da basussukan da Zambia ta ci daga wajenta ba tare da biyan kudin ruwa ba wadanda wa'adinsu ya cika a karshen shekara ta 2005, da habaka yawan kayayyakin da Zambia ke fitarwa zuwa kasar Sin wadanda Sin ba ta buga harajin kwastan a kansu daga 190 zuwa 442, da gina wani yankin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki na kasar Sin a Zambia, da nuna goyon baya ga kamfanonin kasar Sin da su je Zambia don zuba jari, da ba da taimako wajen gina wani filin wasannin motsa jiki a birnin Ndola, da ba da taimako ga Zambia wajen gina wata cibiyar misali ta gwada fasahohin noma, da gina makarantu biyu a kauyuka da asibiti guda da kuma wata cibiyar yaki da cutar malariya a Zambia. Nan gaba, za ta kuma samar da wasu magungunan malariya ga Zambia a ko wace shekara. Daga shekara ta 2007 zuwa ta 2008, gwamnatin kasar Sin za ta bayar da sukolashif ga daliban Zambia 117, za ta kara horar da kwararru iri iri ga Zambia. Za ta kuma tura masanan aikin noma da kuma matasa masu aikin sa kai ga Zambia."

Daga nasa bangaren kuma, Mr.Mwanawasa ya ce, wannan ziyarar da shugaba Hu Jintao yake yi a Zambia da dai sauran kasashen Afirka ta shaida cewa, huldar da ke tsakanin Zambia da Sin wadda aka kulla bisa tushen girmama juna da zumunci da hadin gwiwa tana dinga bunkasa, kuma Sin tana kokarin cika alkawaran da ta dauka a gun taron koli na Beijing na dandalin hadin kan Sin da Afirka. Mr.Mwanawasa ya nuna yabo a kan kokarin da Sin ta yi wajen taimaka wa Zambia wajen daidaita batutuwan zaman al'umma da na tattalin arziki, ya ce,"Har kullum, Sin tana mara wa Zambia baya a kokarin da take yi na neman ci gaba, ciki har da soke basussukanmu, a wannan karo, Sin ta tsai da kudurin soke kudaden bashi da yawansu ya kai dallar Amurka miliyan takwas, a yayin da za ta gina yankin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a Zambia, gaba daya ne za ta zuba kudaden jarin da yawansu zai kai dallar Amurka miliyan 800, wannan zai ba da babban taimako ga Zambia a wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma zai kara samar da guraben aiki da saukaka fatara, zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikinmu. Dukan wadannan ayyukan hadin gwiwa za su sa kaimi ga Zambia wajen tabbatar da shirin bunkasuwa na shekara ta 2000."(Lubabatu)