Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-03 20:20:05    
Hu Jintao ya isa birnin Lusaka don fara ziyararsa a kasar Zambia

cri
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Lusaka, babban birnin kasar Zambia a ran 3 ga wata da yamma bisa agogon wurin don fara ziyararsa a kasar bisa gayyatar da shugaban kasar Zambia Levy Mwanawasa ya yi masa.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai wa Zambia ziyarar aiki, kuma shugaba Mwanawasa ya shirya wani gagarumin biki a filin jirgin sama don maraba da zuwan shugaba Hu.

Shugaba Hu ya yi jawabi a rubuce a filin jirgin sama, cewa kasar Zambia ita ce kasa ta farko da ke kudancin Afirka wadda ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin. Kuma a cikin wadannan shekaru 42 da suka gabata bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, har kullum jama'ar kasashen biyu suna nuna tausayi da goyon baya ga juna da kuma taimaka wa juna, haka kuma sun hada kansu sosai kan tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Shahararriyar hanyar dogo tsakanin kasashen Tanzania da Zambia wani abin tunawa ne ta zumuncin da ke tsakanin Sin da Zambia. Ban da wannan kuma shugaba Hu ya bayyana cewa, nufin wannan ziyararsa a kasar Zambia shi ne hada kai tare da shugabannin kasar Zambia wajen raya zumuncin gargajiya tsakanin kasahen biyu da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninsu da kuma tsara makomar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a nan gaba.(Kande Gao)