Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-03 17:02:42    
Kasashen Zambia da Afirka ta Kudu sun darajanta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka

cri
A gabannin ranar kai ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Hu Jintao zai yi a kasashen Zambia da Afirka ta Kudu, bi da bi ne shugaban kasar Zambia da jami'in kasar Afirka ta Kudu sun darajanta dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin Sin da Afirka.

A ran 2 ga wata, shugaban kasar Zambia Levy Patrick Mwanawasa ya yi bayani a birnin Lusaka, babban birnin kasar, cewa kasar Sin tana son sauraron ra'ayin kasar Zambia, kuma ta samar da dauki ga Zambia a fannoni daban daban don haye wahalolin da ta sha. A waje daya kuma ya karyar da surutun banza na wai sha'awar da kasar Sin ta nuna ga Afirka wani irin mulkin mallaka ne. Kuma ya bayyana cewa, ma'anar mulkin mallaka ita ce kwace albarkatun Afirka da kuma shigad da 'yan Afirka cikin mawuyacin hali. Amma kasar Sin ta zuba kudade masu yawa a Afirka don kago zarafofin aikin yi da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar Afirka.

A ran nan kuma mataimakin ministan harkokin waje na kasar Afirka ta Kudu Aziz Hoosein Pahad ya yi bayani a birnin Johannesburg, cewa ta ganin bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, sauran kasashen duniya za su iya kara fahimtar ma'anar zaman daidai wa daida da samun moriyar juna, da hadin kai don samun nasara da juna, haka kuma za a ba da tasiri ga manufofin da suke bi kan dangantakar da ke tsakaninsu da Afirka.(Kande Gao)