Bayan da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gama ziyararsa a kasar Sudan, ya tashi daga birnin Khartoum, babban birnin kasar a ran 3 ga wata bisa agogon wurin zuwa kasar Zambia don ci gaba da ziyararsa a kasashen Afirka 8.
Shugaban kasar Sudan Omer El-Bashir ya shirya wani gagarumin baki a filin jirgin sama don yin ban kwana da shugaba Hu da 'yan rakiyarsa.
Lokacin da ya yi ziyara a Sudan, shugaba Hu ya yi shawarwari tare da shugaba El-Bashir, takwaransa na kasar, ban da wannan kuma ya gana da Salva Kiir Mayardit, mataimakin shugaba na farko na kasar da kuma Ali Mohammed Taha, mataimakin shugaban kasar, inda suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Sudan da kuma muhimman al'amuran da ke jawo hankulansu. Bugu da kari kuma shugaba Hu ya ziyarci kamfanin sarrafa man fetur na Khartoum wanda kasashen Sin da Sudan suka kafa tare.
Kasar Sudan ita ce zango na uku na wannan ziyarar shugaba Hu a kasashen Afirka 8.(Kande Gao)
|