Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 21:07:37    
Shawarwarin tsakanin Shugaba Hu Jintao da takwaransa Bashir

cri

Ran 2 ga wata, Mr. Hu Jintao shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Sudan ya yi shawarwari tare da Mr. Bashir takwaransa na kasar, inda shugabannin biyu suka yarda da kai dangantarkar sada zumunta irin ta hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu har wani sabon mataki.

Shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, karfafa kuma bunkasa huldar hadin gwiwar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu wata manufa ce da kasar Sin take tafiya. Ya ba da shawara cewa, karfafa hadin gwiwa a zahiri, sami moriyar juna, karfafa hadin gwiwa a karkashin inuwar dandalin hadin gwiwar tsakanin kasashen Sin da Afirka.

Shugaba Bashir ya nuna godiya domin goyon baya da taimakawar da kasar Sin take nuna wa kasar Sudan cikin dogon lokacin da ya gabata kan bunkasuwar tattalin arziki da ta zaman al'umma. Ya nuna cewa, a cikin shekarun baya, an sami nasarori sosai tsakanin kasashen biyu kan hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki, irin wannan hanyar hadin gwiwa ta zama abin koyi.

A cikin shawarwari, shugaba Hu Jintao ya gabatar da matsayin kasar Sin wajen warware matsalar Darfur na kasar Sudan wanda ya kunshe da a girmama ikon mulkin kasa da cikakken yankuna na kasar Sudan,, ya kamata kungiyar Tarayyar Afirka da M.D.D. su taka rawa wadda ta dace kuma mai ma'ana kan batun tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur.. Ban da haka kuma, Mr. Hu Jintao ya ce kasar Sin za ta mayar da kayayyaki masu darajan RMB miliyan 40 ga yankin Darfur.

Mr. Bashir ya nuna godiya ga kokarin da manufofin da kasar Sin take tafiya don goyon baya kasar Sudan ta shimfida zaman lafiya.