Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 19:02:52    
Hu Jintao ya bayar da ka'idojin da bangaren Sin yake bi kan batun yankin Darfur

cri
A ran 2 ga wata, lokacin da yake shawarwari da takwaransa na kasar Sudan Omer al-Bashir, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da ra'ayoyin ka'ida da bangaren kasar Sin yake bi kan yadda za a daidaita batun yankin Darfur cikin lumana. Ya kuma sanar da cewa, kasar Sin za ta samar da kayayyakin agaji da darajarsu za ta kai kudin Renminbi yuan miliyan 40 ga yankin Darfur.

Hu Jintao wanda ke yin ziyara a kasar Sudan ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin yana yaba wa kokarin da gwamnatin Sudan da kungiyar Tarayyar Afirka da kungiyar kawancen kasashen Larabawa da M.D.D. da kuma sauran kasashen duniya da abin ya shafa suke yi wajen daidaita batun yankin Darfur. Ya kuma bayyana cewa, lokacin da ake daidaita batun yankin Darfur, ya kamata a bi ka'idoji kamar su, da farko dai, a girmama ikon mulkin kasa da cikakken yankuna na kasar Sudan. A waje daya kuma, ya kamata a daidaita batun ta hanyoyin yin shawarwari cikin lumana. Haka kuma, ya kamata kungiyar Tarayyar Afirka da M.D.D. su taka rawa wadda ta dace kuma mai ma'ana kan batun tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur. Bugu da kari kuma, ya kamata a inganta halin zaman lafiya da kyautata sharadin zaman rayuwar jama'a na yankin.

Mr. Omer al-Bashir ya nuna godiya ga matsayi da kokarin da gwamnatin kasar Sin take bi domin nuna goyon bayan kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur. (Sanusi Chen)