Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 18:40:52    
Kasashen Sin da Sudan suna raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukan fannoni

cri
Kasar Sudan na daya daga cikin kasashen Afirka da na Larabawa da suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin tun farko. Bayan da suka kulla huldar jakadanci a tsakaninsu yau shekaru 48 da suka wuce, har kullum jama'ar kasashen 2 suna amincewa da juna, suna hada kansu cikin sahihanci, kasashen 2 sun yi ta kara sada zumuncin gargajiya a tsakaninsu. A cikin shekaru misalin 10 da suka wuce, sun sami sakamako da yawa daga wajen yin hadin gwiwar sada zumunci a tsakaninsu, sun habaka hadin gwiwarsu zuwa fannonin siyasa da tattalin arziki da zaman al'umma da al'adu da kiwon lafiya, ta haka jama'arsu sun ci gajiya sosai.

A lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, jakadan kasar Sin a kasar Sudan Zhang Dong ya bayyana cewa, huldar siyasa da ke tsakanin kasashen Sin da Sudan sai danko take samu a ko wace rana, sun kara yin cudanya da juna, sun kuma sami ra'ayi daya kan al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da yawa. Har kullum kasar Sin na goyon bayan kokarin da jama'ar Sudan ke bayarwa wajen tabbatar da sulhuntawar al'umma da shimfida zaman lafiya da wadata a kasarsu da kuma kiyaye mulkin kai da 'yancin kan kasa, sa'an nan kuma ta bai wa jama'ar Sudan goyon baya a kan dakalin kasa da kasa, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta bai wa kasar Sudan tallafi ba tare da son zuciya ba, ba ta tsoma baki cikin harkokin gida na Sudan ba. Kasar Sudan kuwa tana bin manufar kasar Sin daya tak a duniya har kullum, ta mayar da kasar Sin tamkar aminiya ce da ke da dangantaka ta kud da kud a tsakaninsu, kuma ta amincewa da ita. A cikin shekaru misalin 10 da suka shige, manyan jami'an kasashen 2 sun sha kai wa juna ziyara, gwamnatoci da jam'iyyunsu sun yi ta yin cudanya a tsakaninsu. Bayan da ya kawo wa kasar Sin ziyara a shekara ta 1990 da ta 1995, shugaban kasar Sudan Mr. Al-Bashir ya halarci taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a shekara ta 2006, ya kuma sake kawo wa kasar Sin ziyarar aiki. A lokacin nan shugaba Hu Jintao na kasar Sin da Mr. Bashir sun yi shawarwari, inda suka sami ra'ayi daya kan yadda za a kyautata dangantakar hadin gwiwa da abokantaka domin moriyarsu duka.

Haka zalika kuma, kasashen Sin da Sudan sun sami saurin bunkasuwa daga wajen hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki. Kasar Sin abokiya ce mafi girma ga kasar Sudan ta fuskar ciniki, kasar Sudan kuwa abokiya ce ta uku da ta fi yin ciniki da kasar Sin a nahiyar Afirka. A tsakiyar shekarun 1990, kasashen Sin da Sudan sun fara hada kansu a fannin man fetur. Saboda kokarin da bangarorin 2 suka bayarwa tare, a cikin gajeren lokaci ne kasar Sudan ta zama wata kasa da ke samar da man fetur da kuma sayar da man fetur zuwa kasashen waje, a maimakon wadda ta sayi man fetur daga kasashen waje kawai.

Saurin bunkasuwar masana'antun man fetur ya daukaka ci gaban tattalin arzikin kasar Sudan daga dukan fannoni, a sa'i daya kuma, ya sanya kasashen Sin da Sudan su kara bunkasa huldar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu.

Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Sudan a fannin makamashi ya shaida cewa, suna yin hadin gwiwa a tsakaninsu bisa ka'idojin yin zaman daidai wa daida domin moriyar juna da yin hadin gwiwa domin ci nasara tare. Saboda tallafawar da kasar Sin ke ba ta ta fuskar kudi da fasaha, kasar Sudan ta samar da cikakken tsarin masana'antun man fetur cikin sauri. Ba kawai tana iya biyan bukatar kanta a fannin man fetur ba, har ma, tana sayar da wasu zuwa kasashen waje.

Wani babban jami'in ma'aikatar yada labaru ta kasar Sudan ya bayyana cewa, kasashen Sudan da Sin suna fuskantar makoma mai kyau wajen bunkasa huldarsu. Kasarsa ta sami saurin bunkasuwar tattalin arziki da kuma karfafa kwanciyar hankali ta fuskar siyasa saboda hada kai da kasar Sin. A sa'i daya kuma, kasar Sudan ta daga matsayinta a bayyane a nahiyar Afirka da kuma tsakanin kasashen Larabawa da kasashen duniya. Yana fatan kasashen Sudan da Sin za su ci gaba da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, za su habaka hadin gwiwarsu.(Tasallah)