Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 18:08:22    
(sabunta) Hu Jintao ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Sudan

cri
A ran 2 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki na kasar Sudan ya yi shawarwari tare da Omer Al Bashir, takwaransa na kasar, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu, ciki har da warware batun Darfur cikin ruwan sanyi.

Shugaba Hu ya isa birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan ne a ran 2 ga wata da safe bisa agogon wurin. Shugaba al-Bashir shi da kansa ya je filin jirgin sama da kuma shirya wani gagarumin biki don maraba da shugaba Hu da 'yan rakiyarsa. Shugaba Hu ya yi jawabi a rubuce a filin jirgin sama, cewa nan da shekaru 48 da aka kulla huldar diplomasiyya tskanin Sin da Sudan, bangarorin biyu sun samu sakamako mai kyau wajen hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin siyasa da tattalin arziki da cinikayya da al'adu da ilmi da kuma kiwon lafiya, ban da wannan kuma sun yi cudanya da hadin kai tsakaninsu sosai a cikin harkokin duniya. kuma ya yi imanin cewa, ta yin ziyarar, dole ne za a kara zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Sudan, da kuma ciyar da dangantakar hadin kai ta aminci tsakaninsu gaba.(Kande Gao)