Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 19:32:35    
Shugaba Hu Jintao ya gaida dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Sin a Liberia

cri

Aminai makaunata, ko kuna sane da cewa, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya sauka birnin Monrovia, babban birnin kasar Liberia a jiya Alhamis domin yin ziyarar aiki na yini daya a wannan kasa. A lokacin ziyarar, Mr. Hu Jintao ya gaida sojoji da hafsoshin kasar Sin dake aiwatar da babbar dawainiyar wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia.

Kasar Liberia tana yammacin Nahiyar Afrika. Ma'anar sunan kasar ita ce ' walawa'. Amma , wannan kasa ta fada cikin yakin basasa da aka yi daga shekarar 1989 zuwa 2003. A watan Satumba na shekarar 2003, Majalisar Dinkin Duniya ta girke sojojin kiyaye zaman lafiya a Liberia domin yin aikin tsaro. Bisa gayyatar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ne, kasar Sin ta soma halartar yunkurin kiyaye zaman lafiya na aikewa da tawagar musamman zuwa Liberia wanda Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar a watan Disamba na wannan shekara. Wa'adin aikin kowane kashin sojojin, watanni 8 ne. Yanzu, kashi na biyar ke nan na sojojin da suke aiwatar da dawainiyar wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia, wadanda suke kunshe da sojoji da hafsoshi da yawansu ya kai 558. Lallai su ne mafi yawa da gwamnatin kasar Sin ta aike da su bisa babban mataki zuwa wannan kasa.

Da maraicen jiya, shugaba Hu Jintao ya je wurin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suke tsugune a Liberia don gaida su, inda ya duba faratin girmamawa da sojojin suka yi.

' Sannu Abokai' !

'Sannu Shugaba' !

'Lallai kuna fama da aiki' !

'Muna bauta wa jama'a' !

Tun bayan da sojojin kasar Sin suka dauki nauyin kiyaye zaman lafiya a Liberia, lallai sun kawar da wahalhalu da dama a wajen yaki da ciwace-ciwace daban daban da kuma rikice-rikicen zamantakewar al'ummar kasar. A sa'i daya kuma, sun tallafa wa jama'ar wurin wajen gina hanyoyin mota, da haka rijiyoyi ,da gyara filayen jirgin sama da kuma na samar da ruwan sha da wutar lantarki har da ayyukan jiyya.

A watan Nuwamba na shekarar bara, kashi na hudu na dukkan dakarun kasar Sin na wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia sun yi alfaharin samun ' Lambar yabo ta girmamawa ta zaman lafiya' daga Majalisar Dinkin Duniya.

Da yake dakarun kasar Sin suna aiki da kyau, shi ya sa jama'ar wurin suka fadi cewa ' China Good', ' China Good'. Yayin da Mr. Hu Jintao yake duba faratin, ya kuma buga babban take gare su, inda ya furta cewa : 'Tun bayan da kasarmu ta shiga yunkurin kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia a watan Disamba na shekarar 2003, ku abokai ba ku manta da alhakin da jama'ar kasar mahaifa suka danka muku ba, kuma kuna nacewa ga bin ka'idoji da kuma Catar Majalisar Dinkin Duniya. Babu tantama kun taka muhimmiyar rawa wajen zaunar da gindin kasar Liberia da kuma sake gina ta. Saboda haka, jama'ar kasar mahaifa suna alfahari da ku.'

Sa'annan Mr. Hu Jintao ya bayyan kyakkyawan fatansa, cewa: ' Ina fatan za ku dora muhimmiyar dawainiya a gaban komai, da yayata kyakkyawar halayya ta gargajiya, da mayar da hankali kan kiyaye kyakkyawan zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da liberia, da yin ayyuka na-gari ga jama'ar kasar gwargwadon iyawa da kuma sanya kokarin zama manzannin inganta amincin dake tsakanin kasashen biyu'. ( Sani Wang )