Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 16:25:36    
Hu Jintao ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Sudan

cri
A ran 2 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ya isa birnin Khartoum ba da jimawa ba don yin ziyarar aiki a kasar Sudan ya yi shawarwari tare da Omer Al Bashir, takwaransa na kasar, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu, ciki har da warware batun yankin Darfur cikin ruwan sanyi.

Kafin shawarwarin, shugaba al-Bashir ya je filin jirgin sama da kuma shirya wani gagarumin biki don maraba da shugaba Hu da 'yan rakiyarsa.

Shiyyar Darfur tana yammacin kasar Sudan, sabo da an taba yin mulkin mallaka a shiyyar, shi ya sa ta kasance akwai sabane-sabane iri daban daban tsakanin kabilu na shiyyar cikin dogon lokaci, wanda ya yi sanadiyar mutuwa da raunata fararren hula, yayin da mazaunan wurin masu yawa suk yi gudun hijira. A watan Mayu na shekara ta 2006, gwamnatin Sudan da muhimman rukunoni masu adawa da gwamnatin sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Darfur. Kuma a watan Agusta na waccan shekara, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin sanya wa gwamnatin Sudan takunkumi, amma kasar Sin ta kauce wa kada kuri'a. Yanzu gwamnatin Sudan tana yin shawarwari da tattaunawa tare da kasashen waje don warware batun Darfur.(Kande Gao)