Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 21:18:30    
Shugaba Hu Jintao ya fara ziyararsa a Liberia

cri
Ran 1 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka birnin Monrovia, hedkwatar kasar Liberia, inda ya fara ziyarar aikinsa. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai wa kasar Liberia ziyara.

Bayan da ya sauka filin jirgin sama, shugaba Hu ya ba da jawabi a rubuce, inda ya ce, kasar Liberia wata kasa ce mai muhimmanci a Yammacin Afirka. Gwamnati da jama'ar kasar Liberia suna himmantuwa kan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da sa kaimi kan sulhuntawar al'umma, da daukaka sake gina kasa da bunkasuwarsu, da bin manufofin sada zumunci da jituwa a tsakaninsu da kasashe masu makwabtaka da su, da kuma aiwatar da manufofin diplomasiyya daga dukan fannoni cikin himma da kwazo, sun kuma sami sakamako mai kyau. Cikin sahihanci ne jama'ar Sin suke fatan jama'ar Liberia za su sami sabon ci gaba a kan hanyar bunkasuwa.

Mr. Hu ya kara da cewa, nufin ziyararsa a wannan karo shi ne zurfafa zumuncin gargajiya a tsakanin kasarsa da kasar Liberia, da kara fahimtar juna da amincewa da juna, da habaka yin hadin gwiwar moriyar juna, da kuma kara raya dangantakar da ke tsakanin kasashen 2.(Tasallah)