Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 20:28:30    
Aikin kiyaye muhallin da aka yi a lokacin da ake shimfida hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet

cri

Akan kiran tsaunuka masu fadi na Qinghai da Tibet da sunan "tankin ruwa na kasar Sin" ko "kololuwan duniya", matsakaicin tsayin tsaunin daga leburin teku ya kai fiye da mita 4000, yin illa ga halittu masu rai na wannan wuri ba, fadin tuddai da hamada ya kai kusan kashi 3 cikin 4 bisa na duk fadin yankin.

Hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet ta zama hanyar dogo mafi tsawo wadda aka shimfida a kan tsaunukan duniya ta yanzu, a lokacin da kasar Sin take shimfida wannan hanyar dogo, ta bi ka'idar mai da aikin yin rigakafi bisa muhimmin matsayi da ayyukan kiyaye muhalli a gaban kome, cikin ayyukan da aka yi wajen tsara fasali da yin gine-gine da kuma yin zirga-zirgar jiragen kasa, an mai da muhimmanci sosai kan ayyukan kiyaye muhalli da raya halittu masu rai, ta yadda aka sa albarkatun kasa na tsarin halittu masu rai na fadaddan tsaunuka, da tsire-tsire da itatuwan da ke wuri mai sanyi, da tafkuna da wuri mai damshi sun samu kiyayewa.

Domin farfado da itatuwa da tsire-tsire da ke yankunan da aka dauka domin shimfida wannan hanyar dogo, mutane masu binciken kimiyya sun yi bincike kan batun farfado da itatuwa da tsire-tsire da ke kan tsaunukan da ke da dusar kankara, sun yi amfani da fasahar zamani, ta yadda aka sa yawan tsire-tsiren da aka dasa wadanda kuma suka rayu ya kai fiye da kashi 70 bisa 100. A lokacin da aka shimfida hanyar dogo, da farko ma'aikata sun kawar da tsire-tsire daga wurin kuma sun ajiye su a wani wuri daban da kiyaye su da kyau, bayan da suka kammala aikin hakar kasa daga wurin kuma sun sake dasa wadannan tsire-tsire a wurin. An ce, yawan kudin da aka ware domin yin wannan aiki bisa hanyar dogo ya kai kudin Sin fiye da Yuan miliyan 200, fadin filayen ciyayi da aka farfado da su ya kai murabba'in mita dubbai.

Domin kiyaye filayen ciyayi da ke arewacin jihar Tibet, magina masu shimfida hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet sun dasa da kuma canja wuraren filayen ciyayi a kan yankuna masu tsayi wato tsayinsu daga leburin teku ya kai mita 4300 zuwa 4500, wannan ya ba da babban taimako ga kiyaye halittu masu rai da ke bakin hanyar dogo.

A lokacin da aka canja wuraren filayen ciyayi, magina kuma sun kiyaye wurare masu damshi wandanda ake kiransu da sunan "koda na tsaunuka masu fadi" sosai. Domin tabbatar da cewa kada a jawo mugun tasiri ga halittu masu rai na tushen koguna, da kiyaye halittu masu rai na wurare masu damshi sosai, sai a hau da gadoji a wadannan wurare, kuma a haka magudanan ruwa a kwaruruwa, da gina kananan gadoji da yawa maimakon hanyar da aka shimfida a duk wuraren da ake bukata.

Bayan da aka tsabtace gurbataccen ruwa na masana'antu da na zaman yau da kullum, an yi amfani da su don shayar da bishiyoyi da rage kura, an hana zubar da su cikin koguna sosai, wannan ya kawo amfani wajen yin rigakafi ga kazancewar albarkatun ruwa da wurare masu damshi.

A fannin kiyaye muhallin tafkuna na tsaunuka masu fadi kuma, aikin kiyaye tafkin Cuona ya gwada misalin koyo wajen kiyaye tafkunan da ke bakin hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet. Tafkin Cuona yana cikin gundumar Anduo ta jihar Tibet, fadinsa ya kai fiye da kilomita 400 wanda mutanen wuri ke ba shi sunan "tafki mai tsarki". Magina hanyar dogo sun kiyaye wannan tafki mai ruwan dadi da kyau ta hanyar gina bangwaye da canja wuraren filayen ciyayi da sauransu.